TARIHIN ALHAJI ABUBAKAR QUDUS ( 1891 - 1967)
- Katsina City News
- 17 Dec, 2023
- 679
Daga Kasim Batagarawa
Alhaji Abubakar Qudus dan Muhammadu Datti (farkon limamin garin Batagarawa) ɗan Ummaru Kaki ɗan Muhammadu ɗan Ahmadu.
Alhaji Abubakar Datti da aka fi sa ni da Alhaji Qudus ko Alhaji Abubakar Qudus, an haife shi a shekarar 1891 a kauyen Kwami, karamar Hukumar Batagarawa, Jihar Katsina. Ya kasance daya daga cikin jikokin malaman Batagarawa (Limaman Batagarawa) wato mutanen Kwami. Babban Malami ne mai son yawan neman ilimi da kasuwanci. Malami ne wanda tun tasowar sa ya ba neman ilimin addini da koyar dashi muhimmanci a rayuwar shi. Ganin haka ne ya sa wansa Alhaji Hamza da yayi niyyar tafiya aikin hajji ya yi shawarar tafiya da shi Ƙasar Makka don sauke farali da kuma taimaka masa wajen hidimomin da ke cikin tafiyar.
Bayan isar su Birnin Makka ne Allah ya yi ma Alhaji Hamza rasuwa a shekarar Dubu daya da dari tara da tara (1909), lokacin Abubakar yana kamar dan shekara 18 bai san yadda zai dawo gida ba. Lura da damar samun ilimin arabiyya da na islama sai ya zabi zama garin Makkah don ci gaba da neman ilimin sa. Hakan ya bashi damar haduwa da kuma samun ilimin addini wajen Malamai daban- daban na duniya dake zuwa kasa Mai tsarki don aikin hajji da wasu hidimomin.
Ya yi shekara goma (10) a birnin Qudus (Inda ya samu Lakanin Qudus) sanadiyar shiga aikin soja tare da Hukumar kasar Saudiya don bada gudummuwar shi ga Ƙasar Palestine a yaƙin da suka yi da Yahudawan Isra'ila.
Bayan an ƙare yaƙi sai Malam Abubakar Qudus ya dawo Ƙasar Misra (Egypt) don ci gaba da neman ilimin shi wajen malaman kasar, musamman wadanda ya hadu da su a Palastine da kuma Makka.
A nan Ƙasar Misra ne a wata ziyara da Sir Ahmadu Bello ya kai, ya gan shi yana koyar da karatu sai ya kwadaitu da iliminshi, yace lallai sai ya maido shi gida a amfane shi, daga nan ne Sir Ahmadu Bello ya dawo da shi gida Nigeria ya hallarta ma Sarkin Katsina Muhammadu Dikko shi don cin gajiyar ilimin shi.
Sarkin Katsina Muhammadu Dikko kuma ya gina masa gida a Rafindaɗi, aka kuma aura masa Maimunatu ɗiyar Waziri Zayyana suka haifi diya daya Hadiza. Ya kuma auri Halimatu (Ma'inna) diyar gidan Liman Kasimu a garin Rimi.
Sarakunan Katsina Muhammadu Dikko da Sir. Usman Nagogo sun yi tarayya ƙwarai da gaske da Abubakar Qudus, bayan neman fatawa da karatun addini, Sarakunan suna neman shawarwari kan sha'anin mulki da kuma wasu abubuwa sabbi da kan bijiro.
Saboda kyakkyawar alakar su lokacin da Sarautar Rawayau da ta Gotomawa suka faɗi, Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo ya buƙaci Alhaji Abubakar Qudus da ya bi Malam Buhari (wanda ƙane ne ga Sarki Muhammadu Dikko) su tafi ya raka shi Rawayau don su yi mulkin Rawayau da Gotomawa don bada tashi gudummuwar ta koyar da addini, Abubakar Qudus ya faɗa wa Mai Martaba Sarki cewa, ayi mashi uziri saboda ai shi ba mai zama ba ne, sai dai ƙanensa Muhammadu Madani ya bi shi.
Sai Muhammadu Madani ya raka malam Buhari Rawayau don yin mulkin Rawayau, shi kuma Muhammadu Madani ya yi mulkin Gotomawa a Matsayin Galadima.
Alhaji Abubakar Qudus ya zauna a Rafin daɗi, yana kuma dinga shiga kauyuka irin su Bakiyawa da Rawayau da Batagarawa yana karantar al'umma addinin musulunci.
Ya yi yawace - yawace neman ilimin addini kasashe da dama irin su Saudiyya da Sudan da Istanbul da Sham da Bagadaza da Misira da Qudus da Jordan. Ya yi mafi yawan neman ilimin tare da ɗansa Khadi Abdulkadir Abubakar Qudus Rafin dadi wanda Mallamawa Dikko a shekarar 2001 ya naɗa a matsayin Dan- masanin Batagarawa.
A shekara ta Dubu daya da dari tara da hamsin da biyu (1952) ya dawo gida Katsina baki ɗaya ya zauna gidansa na Rafin ɗaɗi, wanda ya kasance yana koyar da karatun addinin musulunci, gidan kuma ya zama masauki ga malaman dake kawo mashi ziyara daga kasashen da yaje neman ilimi, haka ma gidan shi ya zama masaukin yan'uwa da abokan arzuka musamman lokutan bukukuwan Sallah babba da karama ko na Maulidi, inda dangi daga Ɓatagarawa da sauran wurare kan je su sauka don murnar shagalin sallah.
Shima ya gina Rijiya nan kusa da Madugu House Ƙofar Ƙwaya Katsina a lokacin rayuwar shi a matsayin sadaƙatul - jariya kamar yadda Kakannin sa suka yi a garin Batagarawa.
Ya rasu a Kano a ranar Litinin 15-1-1967 yayin da ya kai wata ziyara ga ƴan'uwansa da ke Kano. Ya haifi ƴaƴa kamar haka: Fatima da Hadiza da Abdulƙadir da Sa'adiya da Abdu'aziz da Hau'wa'u.