NAGA YADDA AKE SAFARAR MUTANE ZUWA KASAR IRAQ
- Katsina City News
- 26 Sep, 2023
- 797
@Katsina Times
Jaridar Taskar Labarai
Wannan hoton da kake gani a sama.Ba wani gari bane a kudancin Najeriya. Wasu kabilu ne, yan kudancin Najeriya sun fi su dari da mukayi, arba dasu a filin Jirgin Birnin Cairo ta kasar Masar, zasu tafi kasar Iraq neman kudi.
Nayi magana da jagorar su, ta shaida mani cewa, wani kamfani a legas ya kwaso su ya dau nauyin zuwan su, zasu yi aiki na shekaru biyu sannan su dawo Najeriya.
Ta fada mani cewa, sun fito daga jihohin kasashen yarbawa ne, ta fada mani cewa zasu shekara daya suna biyan kudin da aka kashe masu, sannan su shekara daya suna tara abin da zasu dawo Najeriya dashi.
Na tambaye ta irin neman kudin da zasu rika yi tace duk abin da ya samu.
Shugabar tasu ta fada mani ita Kirista ce, sunan ta na yanka Deborah amma sunan ta na tafiya zuwa kasar Iraq Aishat, kuma haka kowa ya chanza sunan shi a tawagarta mai mutane 120.
Tace Jirage uku suka biyo zuwa Iraq, wasu suka taso daga Abuja, wasu Kano wasu Legas, duk don batar da sau.
Amma a Cairo jirgi daya muka hau zuwa Baghdad, mun sauka har Baghdad tare anan Filin Jirgin muka rabu.
@ www.katsinatimes.com
@ www.jaridartaskarlabarai