Wanda Ya Fi Kowa Yawan Mabiya A TikTok Musulmi Ne Kuma Hafizin Ƙur'ani
- Katsina City News
- 09 Sep, 2023
- 909
A shekarar da ta gabata ne Khaby Lame, mutumin da ya fi kowa yawan mabiya a dandalin TikTok, ya bayyana addininsa yayin wata tattaunawa. Yayin da yake bayar da amsa a kan tambayar da ake yawaita yi masa game da addininsa, ɗan TikTok ɗin mai shekaru 22 ya bayyana cewa shi Musulmi ne kuma hafizin Al-Ƙur'ani.
Khaby Lame ya bayyana cewa an haife shi a ƙasar Senegal a ranar 9 ga watan Maris, 2000. Bayan ya cika shekara ɗaya a duniya iyayensa suka koma ƙasar Italiya da zama. A lokacin da ya cika shekaru 14 sai suka tura shi makarantar koyan Al-Ƙur'ani a kusa da Dakar, Senegal, inda ya koyi karatun Al-Ƙur'ani mai tsarki, sannan ya zama hafizi, ma'ana mahaddacin Ƙur'ani.
Ɗaukakar Khaby ta fara a lokacin da ya rasa aikinsa na kamfani a Italiya a watan Maris 2020 sakamakon annobar cutar COVID-19. Mahaifinsa ya yi ta ƙarfafa masa gwiwa kan ya nemi wani aikin amma sai Khaby ya sadaukar da sa'o'i da dama wajen ƙirƙirar bidiyoyi da wallafa su a dandalin TikTok a kullum.
Abin da ya bambanta Khaby da sauran masu wallafa bidiyo a TikTok shi ne yana wallafa bidiyon barkwanci mai nuna yadda za ka aikata wasu ayyuka masu wahala ta hanyar bin hanya mafi sauƙi. Ya kuma kasance yana nuna hanyoyin masu sauƙin ba tare da furta kalma ko ɗaya ba. Hakan ne ya sa Khaby ya shahara har ya tara mabiya miliyan 145.6, sannan rahotanni suka bayyana cewa ya mallaki kuɗi kimanin dala miliyan biyu.
A ranan 22 ga watan Yuni, 2022, Khaby ya zamo wanda ya fi kowa yawan mabiya a TikTok inda ya wuce Charli D'Amelio, wanda yake da mabiya miliyan 142.1 a lokacin.
Fassarawa: Yasir Kallah