Dantakarar Shugaban Karamar Hukumar Katsina Ya Kammala Rangadin Mazabu 12

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12022025_181559_Screenshot_20250212-190240.jpg


Katsina, 12 ga Fabrairu 2025 – Dantakarar kujerar shugabancin Karamar Hukumar Katsina, Honorabul Isah Miqdad AD Saude, ya kammala yakin neman zabensa a mazabun birnin Katsina guda 12 da suka hada da Kudu II, Kudu III, da Gabas II.

A yayin kammala rangadin nasa, manyan jiga-jigan siyasa da dattawan yankin sun tarbe shi, ciki har da kansilolin mazabu da dattawan siyasa irin su Alhaji Kabir KSƘ, Kabir Amoga, Amb. Yaqub, tsohon shugaban karamar hukumar Katsina, Alhaji Bala Saulawa, da Dr. Idris Zakari. Hakazalika, Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Katsina, Honorabul Sani Aliyu Danlami, da Shugaban Kungiyar Dillalan Manfetur, Alhaji Aminu Wali (A A Rahamawa), sun halarci taron goyon baya ga dan takarar.

Taron yakin neman zaben wanda aka fara a ranar 9 ga Fabrairu ya gudana ne a mazabun Kangiwa, Arewa ‘A’ da Arewa ‘B’, sannan ya ci gaba da ziyara a yankunan Shinkafi, Gabas I, da Kudu I. Ya zuwa ranar Laraba 12 ga Fabrairu, Isah Miqdad ya karkare rangadinsa a mazabun Kudu II da Gabas II, inda ya jaddada kudirinsa na kawo ci gaba da bunkasa yankin idan aka zabesa.

Ya bayyana godiyarsa ga jama’a bisa irin goyon bayan da suke ba shi tare da alkawarin samar da nagartattun ayyuka idan ya samu damar jagorantar karamar hukumar.

Yakin neman zaben ya gudana ne karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Katsina, tare da halartar dimbin magoya baya da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa na yankin.

Follow Us