APC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zaben Shugaban Karamar Hukumar Katsina da Kansiloli 12

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

A ranar Laraba, 28 ga watan Janairu, 2025, jam’iyyar APC ta gudanar da gangamin kaddamar da yakin neman zaben shugaban karamar hukumar Katsina (Katsina Municipal) da kansilolinta 12. An gudanar da taron ne a filin Masussuka da ke Kofar Soro, cikin birnin Katsina, inda dubban magoya bayan jam’iyyar suka hallara domin nuna goyon bayansu.  

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigai daga jam’iyyar APC, ciki har da shugabannin jam’iyya daga matakai daban-daban, ‘yan siyasa, da kuma masu ruwa da tsaki a harkokin dimokuraɗiyya. A lokacin taron, an mika tutar jam’iyyar ga dan takarar kujerar shugaban karamar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, tare da kansilolinsa 12, lamarin da ya tabbatar da cikakken shirin APC na fafatawa a zaben kananan hukumomin da za a gudanar a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025, a fadin jihar Katsina.  

A jawabinsa bayan karbar tutar jam’iyyar, Hon. Isah Miqdad AD Saude ya bukaci al’ummar Katsina da su mara masa baya domin ci gaba da kawo ci gaba da sauye-sauye masu amfani. Ya jaddada cewa jam’iyyar APC ta kuduri aniyar inganta rayuwar al’ummar gari, tare da ba da fifiko ga matasa da mata, kasancewar su ne ginshikin dimokuraɗiyya.  

"Tabbas, matasa da mata su ne jigon ci gaban kowace al’umma, don haka tsarin shugabancina zai fi karkata ga tallafa musu domin bunkasa rayuwarsu," in ji shi.  

Hon. Isah ya kuma bukaci dukkanin ‘ya’yan jam’iyyar APC da su fito kwai da kwarkwata domin kada kuri’unsu a ranar zabe, tare da tabbatar da nasarar jam’iyyar a matakin karamar hukuma. Ya ce, “Wannan lokaci ne da ya kamata mu hada kai domin tabbatar da ci gaban gari. Kada mu bari kowace jam’iyyar adawa ta yi mana zarra. Mu fito mu kada kuri’a domin tabbatar da nasarar APC.”

Gangamin yakin neman zaben ya gudana cikin tsari, inda mahalarta suka nuna kwarin gwiwarsu tare da yin alkawarin bai wa jam’iyyar cikakken goyon baya domin cimma nasara a zabe mai zuwa.

Follow Us