"BAN CE NA GOYI BAYAN ƘUDIRIN GYARAN DOKAR HARAJI ƊARI BISA ƊARI BA: INA BADA HAKURI NA RASHIN FAHIMTA -Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa
- Katsina City News
- 04 Dec, 2024
- 182
Ina jan hankalin al'ummar ƙananan hukumomin Ƙiru da Bebeji, Jihar Kano, Arewa da Nigeria cewa BABU WURIN DA KO SAU ƊAYA NA CE INA GOYON BAYAN SABABBIN DOKOKIN HARAJI ƊARI BISA ƊARI.
Abin da nace, akwai batutuwa da dama waɗanda za su zama alheri ga Arewa da Nigeria. Kuma mu yan Majalisa na yankin arewa mu yi amfani da rinjayen da mu ke da shi a majalisa, mu tsaya daram mu goyi bayan duk wasu ƙudirorin da za su amfani Arewa ta fannonin bunƙasa tattalin arzikin yankin, waɗanda ke cikin ƙudirorin. Mu kuma cire waɗanda za su cutar da mu ko mu gyarata a yadda ba za ta cutar da mu ba.
Kuma mu yi amfani da wannan damar dokar da aka kawo mu bijiro da wasu sabbi da muka tabbatar za su amfani Arewa, domin a shigar da su a cikin kundin ƙudirorin. A yayin haka kuma, mu tabbatar da yi wa sauran jihohi da yankunan Nigeria adalci a tsarin dokar. Amma ra'ayin wasu shi ne a yi watsi da dokar gaba ɗaya.
A matsayi na na mai hawa huɗu a Majalisa, ban taba kuma ba zan taɓa goyon bayan duk wata doka ko ƙudirin da zai kawo illa ga mazaɓa ta, jihata Kano ko Arewa dama Nigeria ba.
AMMA DUK DA HAKA INA BAIWA DUK WAƊANDA MATSAYANA AKAN DOKAR YA ƁATA MUSU RAI. Da 'yan uwana 'Yan Majalisar wakilai, Sanatoci, Gwamnoninmu, Shugabanninmu, Sarakunanmu, Malamanmu, 'yan kasuwanmu, 'yan siyasa, 'yan bokonmu, yan jaridunmu, mata da matasa da duk jama'armu baki ɗaya.
Musamman Ubana Jagoran NNPP/Kwankwasiyya SENATOR RABIU MUSA KWANKWASO PhD, FNSE da irin shawarwarin da ya bani. A nan zan haɗa da ALƘALI SALIHU ABUBAKAR NAJAMILA ZARIA kan jajircewa wajen faɗakarwa. Allah (SWT) Ya yi musu albarka, amin.
INA KUMA BADA TABBACI CEWA ZAN YI DUK ABIN DA ZAN IYA YI, IYA ƘARFIN ƊAN ADAM IN GA CEWA BA A CUTAR DA AREWA BA DA KUMA GANIN AN YI WA KOWA ADALCI A NIGERIA, A KOWANE LOKACI KAMAR YADDA NA SABA YI.
Allah ya taimaki Ƙiru/Bebeji, Jihar Kano, Arewa da Najeriya baki daya amin."
Naku har abada.
Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa PhD Kiru/Bebeji, Kano
(Jarman Bebeji)
04/12/2024