Kamfanonin Sadarwa Sun Biya Harajin Naira Tiriliyan 2.5 Ga Najeriya a Rabin Farkon Shekara – NITDA

top-news

Katsina Times 

Hukumar Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) ta bayyana cewa kamfanonin fasahar sadarwa na ƙetare, ciki har da X, Google, Microsoft, da TikTok, sun biya haraji da ya kai Naira tiriliyan 2.55 ga gwamnatin Najeriya a rabin farkon shekarar 2024 (H1 2024).  

Wannan bayanin ya fito ne cikin wata sanarwa da Hadiza Umar, Daraktar Sadarwa da Hulɗar Jama’a ta NITDA, ta fitar a ranar Talata. Ta ce, bisa ga bayanan Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS) da Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS), wadannan kamfanonin sadarwa sun bayar da gudummawar da ta haɓaka kuɗaɗen shiga ƙasar.  

Hukumar ta NITDA ta yaba wa waɗannan kamfanoni saboda bin dokar gudanar da dandalin sadarwa ta intanet da ka’idojin kare lafiya da tsaron masu amfani da dandamali.  

Sanarwar ta kara da cewa dokar, wacce aka samar tare da haɗin gwiwar Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) da Hukumar Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC), ta ƙunshi matakai na tabbatar da tsaron intanet da magance matsalolin da ke da alaƙa da abubuwa marasa kyau.  

A cewar NITDA, “Bayanan Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS) da Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) sun nuna cewa kamfanonin sadarwa na ƙetare, ciki har da dandamalin sada zumunta da sauran masu ba da hidimar intanet, sun bayar da harajin da ya kai Naira tiriliyan 2.55 (kimanin dala biliyan 1.5) a rabin farkon shekarar 2024.”  

Hukumar ta bayyana cewa wannan ci gaban ya nuna muhimmancin kyawawan manufofin tsari a fannin fasahar sadarwa wajen samun haɗin kai daga kamfanoni da kara samar da kuɗaɗen shiga.  

Bugu da ƙari, NITDA ta bayyana cewa akwai ci gaba a matakin da fafafen suka dauka don tabbatar da tsaron masu amfani da bin dokokin da aka gindaya musu. Hukumar ta ce an samu rahotannin ƙorafe-ƙorafe har miliyan 4.1 a shekarar 2023, inda aka cire abun ciki miliyan 65.8 daga dandalin, yayin da aka sake wallafa wasu abubuwa 379,433 bayan sake nazari.  

“Dandalin sadarwa sun karɓi ƙorafe-ƙorafe guda 4,125,283 a shekarar 2023,” in ji sanarwar NITDA. “An rufe da kuma soke asusun masu amfani har guda miliyan 12.09.”  

NITDA ta yaba da ci gaban da aka samu, amma ta ce akwai buƙatar ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da sabbin dabaru don magance ƙalubalen fasahar sadarwa a nan gaba.  

Hukumar ta yi kira da a samar da yanayi mai tsaro da ɗabi’a a fagen fasahar sadarwa.