TARIHIN SARAUTAR MUTAWALLI A MASARAUTAR KATSINA.
- Katsina City News
- 25 Nov, 2024
- 443
Sarautar Mutawalli ta samo asalintane a lokacin Mulkin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko(1906-1944). Acikin shekarar 1907, aka bude Baitil Mali na farko a Arewacin Nigeria a Katsina ( First Treasury in Northern Nigeria). A sabili da hakane sai Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya zabo wani daga cikin aminnan shi, ya nadashi Sarautar Mutawalli watau, Mai kula da Baitil Mali a Masarautar Katsina. Mutum na farko da aka fara nadawa wannan Sarautar shine Mutawalli Ummaru. Mutawalli Ummaru shine Mahaifin Alhaji Musa Yar'adua, Kuma kakan Alhaji Ummaru Musa Yar'adua, ( Shugaban Kasar Nigeria) da General Shehu Musa Yar'adua da sauransu. Aikin Mutawalli a wannan lokacin shine kula da Baitil na Katsina Kuma tattara ajeye kudaden da aka Tara na Haraji dana Kasuwa. Mutawalli Ummaru yayi Sarautar Mutawalli daga shekarar 1907 zuwa 1911. Bayan rasuwar sane sai Kuma aka nada Mutawalli Sayyadi Gafai.
2. MUTAWALLI SAYYADI GAFAI. Shine Mutawalli na biyu a Katsina. Mutawalli Sayyadi Yana daga cikin zuruar Malam Yahaya Gafai, yanzo yazo Katsina daga Yandoton Tsahe wajen shekarar 1767, Yana daya daga cikin Malaman Jami'ar Yandoto a wancan Lokacin da shi da mahaifin shi Malam Buhari. Mutawalli Sayyadi shine ya haifi Hajiya Dada Mahaifiyar Shugaban Kasar Nigeria da Shehu Yar"adua da sauransu. Daga Mutawalli Sayyadi sai Kuma Mutawli Balarabe.
3. MUTAWALLI BALARABE. Ya fito ne daga Unguwar Masanawa dake cikin Unguwannin birnin Katsina. Alhaji Abbas Masanawa Wanda yayi takarar Gwamna Katsina a Jamiyyar Apc Yana daga cikin zuruar shi. Daga Mutawalli Balarabe sai Mutawalli Sule.
4. MUTAWALLI SULE. Shi Kuma Dan Kusada ne, Kuma cousin ne ga Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo. Ya zauna Unguwar Yarinci Katsina. Bayan rasuwar Mutawalli Sule sai Kuma Sarautar Mutawli ta koma Gidan Mutawalli Ummaru inda aka nada Alhaji Musa Yar'adua a matsayin Mutawallen Katsina.
5. MUTAWALLI MUSA YAR'ADUA. Shi Alhaji Musa Yar'adua a lokacin Yana Tafidan Katsina sai ya sabka daga Sarautar Tafida aka ba danshi Musa Yar'adua shi Kuma aka nadashi Mutawallin Katsina. Shi Musa Yar'adua dane ga Mutawallin Katsina na farko watau Mutawlli Ummaru. An haife shi a shekarar 1912. Yana daga cikin daliban Katsina College na farko, Wanda ya halarceta daga shekarar 1925 zuwa 1930. Yayi aiki da NA ta Katsina. Daga baya ya shiga Siyasa, inda takai har ya rike Ministan Lagos a Jamhuriya ta daya. Shi Mutum ne Mai kishin addini, Wanda ya zuwa karshen rayuwarshi Yana bada sadaka ga marasa karfi( Talakawa ) a kofar Gidan shi. Daga cikin yayan shi da sukayi Sarautar Mutawalli akwai.
6. ALHAJI UMMARU MUSA YAR',ADU ( MUTAWALLI) Sai Kuma Mutawalli na yanzu watau,
7. SENATOR ABDULAZEEZ MUSA YAR'ADUA.
..
Har ya zuwa yanzu zuruar Mutawalli Ummaru sune suke rike da wannan Sarautar Mutawalli.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.