GIDAJEN MAN ƊANMARNA NA SAYAR DA MANSU DA SAUƘI A KATSINA
- Katsina City News
- 05 Nov, 2024
- 281
Daga Muhammad Ali Hafiz
@ Katsina Times &
Jaridar Taskar labarai
Binciken da jaridun Katsina Times suka yi a babban birnin jihar Katsina da kewaye, ya gano rukunin gidajen ƊANMARNA suna sayar da man fetur da sauƙi fiye da sauran gidajen man da ake da su, kuma suke bayar da mai a Katsina.
Jaridun Katsina Times sun gano gidajen man MATRIX, ADMAN, HIMMA, AL-HAYAT, AL-RAHAMAN, CON OIL da SHEMA PETROLEUM, duk suna sayar da fetur ɗinsu ne a kan Naira dubu ɗaya da dari ɗaya da hamsin a kan kowace lita (1150).
ALMU'AZZAM kuma yana sayarwa ne a kan Naira dubu ɗaya da ɗari ɗaya da arba'in a kan kowace lita.
TOTAL ENERGIES kuma yana sayarwa a kan Naira dubu ɗaya da ɗari ɗaya da arba'in da tara, yayin da GWAGWARE INTERNATIONAL LIMITED ke sayarwa a kan Naira dubu ɗaya da ɗari ɗaya da tamanin.
Amma rukunin gidajen man ƊANMARNA a gidajen mansa shida da muka ziyarta a hanyar Dutsinma da titin IBB da gadar Ƙofar Ƙaura da Ƙofar Durɓi da kuma sabon titin kwaɗo da bayan tsohuwar CBN, duk suna sayarwa ne a kan Naira dubu ɗaya da ɗari ɗaya da ashirin 1120
A binciken Katsina Times a satin da ya gabata zuwa yammacin Litinin 3 ga watan Nawumba, 2024, babu wani gidan man da ya kai na ƊANMARNA sauƙi da kuma araha, kuma ga man ya wadata a duk gidajen mansu guda shida da muka ziyarta.
Bincikenmu ya tabbatar DANMARNA yana daga cikin manyan dilolin mai yanzu a ƙasar nan, kuma duk wahala da halin da man fetur zai shiga yana fifita jihar Katsina ganin cewa ya samar masu da man fetur a lokacin da ake wahalarsa.
Bincikenmu ya gano lokacin da aka yi kwanaki ana zanga-zangar tsadar rayuwa duk da hatsarin da ake ciki, gidajen mai da yawa sun rufe, amma ƊANMARNA ya riƙa ba da mai ga masu buƙata don kar wahalar ta yi yawa.
Rukunin gidajen man ƊANMARINA da ke da rassa a duk faɗin ƙasar nan, ya samar wa da dimbin mutane aikin yi a ciki da wajen jihar Katsina.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
Www.katsinatimes.com
Da duk shafukan sada zumunta na social media