BARAYIN DAJI SUN HANA MUTANEN MAIDABINO CIN KASUWA A DANMUSA
- Katsina City News
- 22 Oct, 2024
- 312
...Sun kai hari gari tsamiyar jino a kankara
Muazu Hassan @ Katsina Times
A yau talata 22 ga oktoba barayin Daji suna hana Mutanen garin Maidabino dake karamar hukumar Danmusa cin kasuwar garin Dan musa da kuma kankara.
Barayin sun tare hanyar da ita kadai ce Mutanen garin na Maidabino ke amfani da ita wajen cin kasuwannin garin DanMusa da kuma kankara.
Tsawon lokaci barayin daji sunyi wa Mutanen Maidabino kawanya basa iya fita garin,daga sati sai kuma wani satin,Wanda yake ranakun kasuwa ne lokacin suke amfani dashi su fita suje kasuwanni da rakiyar jami an tsaro su sawo abin bukatar da zai kai su har wani sati.
A yau talata barayin sunyi fitar da jami an tsaron basu iya tunkarar su har Sufi karfinsu su kai mutane kasuwa su maido su.
Wasu mutanen garin da jaridun Katsina Times sukayi magana dasu sun fada mana cewa zasu yi zaman kunci a wannan satin mai zuwa .
Sunce komai ya kare , fatan suje kasuwa su sawo yanzu babu zuwa kasuwa.Barayin sun fito da yawan gaske Wanda har sun tare wasu motocin da suka fara safkon fitowa.jaridun Katsina Times basu samu tabbacin me ya faru ba.
Barayin dajin sun kai Hari garin yar tsamiyar jino dake karamar hukumar kankara, Rahotanni na cewa an kashe mutanen gari da sace wadansu da tafiya dasu daji.
Jaridun Katsina Times sun samu magana da wasu mutanen garin na tsamiyar jino wadanda suka fada mana cewar barayin sun yi masu kawanya ne , sannan suka fara afka ma jami an tsaron dake garin, bayan sun ga sun ci karfin jami an tsaron sai suka fada ma mutanen gari.
Munyi kokarin jin ta bakin rundunar yan sanda amma ba muyi nasara ba.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
All in All social media handles
07043777779 08057777762