Gwamnatin Katsina Ta Ba Da Tallafin Buhunan Shinkafa 40 Ga Gidan Marayu Da gidan gyaran Hali
- Katsina City News
- 17 Sep, 2024
- 194
Gwamnatin Jihar Katsina ta ba da tallafin buhunan shinkafa 40 ga Gidan Marayu na Atta’awan dake Dandagoro da Gidan Gyaran Hali na Remand Home a cikin garin Katsina, a matsayin wani bangare na kokarinta na tallafawa al’umma.
A ranar Talata, 17 ga watan Satumba, 2024, kwamiti da gwamnatin jihar Katsina ta kafa, karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Abdullahi Garba Faskari, ya raba buhunan shinkafa 20 kowanne ga wadannan wurare guda biyu.
Wadanda suka halarci rabon sun hada da Barista Abdullahi Garba Faskari, Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi, Dakta Ahmad Filin Samji, wakilan masarautun Katsina da Daura, jami'an Hukumar Hisbah, kungiyoyin farar hula, Hukumar Tsaro ta DSS, 'yan sanda, da wasu jami’an gwamnati da wakilan kungiyoyin addinai.
A cewar Sakataren Gwamnatin Jihar, wannan tallafin na daga cikin buhunan shinkafa 24,000 da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar Katsina don rage talauci. Ya kuma jaddada cewa gwamnatin na ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen tallafawa al’umma.
Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi, Dakta Ahmad Filin Samji, ya nuna godiyarsa ga gwamnatin, ya kuma yaba da wannan taimako, inda ya bayyana cewa Gidan Marayu na Atta’awan yana samun tallafi daga gudummawar al’umma da shirin koyar da sana’o’in hannu ga marayun da suke kula da su.
Haka, yayin ziyarar Gidan Gyaran Hali na Remand Home, shugaban cibiyar, Aliyu Galadima, ya nuna godiyarsa kan wannan tallafi, tare da yin addu’o’in fatan alheri ga Gwamnatin Jihar Katsina da gwamnatin tarayya kan kyautatawar da suke yi wa al’umma.