Tatsuniya Ta 37: Labarin Yar Mowa Da 'Yar Bora
- Katsina City News
- 12 Jul, 2024
- 804
Ga ta nan, ga ta nanku.
A wani gari an yi wani mutum mai mata biyu da 'ya'ya biyu, 'yan mata; daya sunanta 'Yar Mowa, dayar kuma 'Yar Bora. Suna nan, ran nan sai mijinsu ya rasu. Bayan dan wani lokaci kuma sai uwar 'Yar Mowa ta rasu, ta bar uwar 'Yar Bora kadai. To da ma kafin ta rasu, ta kira kishiyarta ta ce mata: "Don Allah ga amanar yata nan; ki kula da ita." Sai ta ce: "To."
Amma da ta rasu sai uwar 'Yar Bora ta fara gana wa 'Yar Mowa azaba. Kullum ita ke yin hidimar gida, ba ta da lokacin hutawa. Wata rana da gari ya waye sai aka ga 'Yar Bora ta yi fitsarin kwance, amma sai uwar 'Yar Bora ta ce ai 'Yar Mowa ce ta yi. Saboda haka ta matsa mata sai ta je Rafin Bagaja ta wanke shimfidar da aka yi wa fitsari.
To Ruwan Bagajar nan kuwa yana cin mutane. Amma tun da ba yadda ta iya, sai ta dauki shimfida ta kama hanyar rafi. Tana cikin tafiya a daji da ta ga rafi sai ta kama waka tana cewa:
"Kogi, kogi,
Ko kai ne Ruwan Bagaja,
Bagajar kauye da 'Yar Sarki,
Da 'Yar Bora ta yi fitsari,
Aka ce ni ce,
Sai na wanke
A Ruwan Bagaja."
Sai kogi ya ce: "Ni ba ni ne Ruwan Bagaja ba. Ni Ruwan Madara ne. Ki zauna ki sha to." Sai ta ce ta gode; ta ci gaba da tafiya. Can sai ta tarar da wani ruwan, sai ta sake maimaita wakar da ta yi. Sai kogi ya ce mata shi Ruwan Zuma ne. Idan tana so ta zauna ta sha. A nan ma ta ce ta gode, ta ci gaba da tafiya. Sai ta tarar da Kogin Shinkafa da Kaji, sai ta rera wakar nan, kogi ya ce mata: "Ni Kogin Shinkafa da Kaji ne. Idan kina so ki zauna ki ci."
A nan ma ta yi godiya, ba ta ci ba; ta yi gaba. Jim kadan kuma sai ta tarar da Ruwan Jini. Bayan ya ji eikin waka, sai ya ce: “Ni ba Ruwan Bagaja ba ne. Ni Ruwan Jini ne. In za ki sha to." Sai ta ce ta gode ta yi gaba. 'Yar Mowa dai ba ta gaji ba, ta ci gaba da tafiya har ta tarar da wani ruwan. Da ta yi irin wakar da ta saba sai ya ce: "Ni ne Ruwan Bagaja; amma ke kuwa wannan yarinya me ya kawo ki wurina inda ba a zuwa?" Sai ta fede masa biri har wutsiya a kan abin da ya faru da irin halin da take ciki bayan rasuwar mahaifiyarta. Da Ruwan Bagaja ya ji sai ya ce: "To ai sai ki wanke a nan."
Nan take ta yi godiya, ta tsuguna ta wanke shimfida, amma kafin ta gama har dare ya yi. Da ta gama, ta tashi za ta tafi sai kuma ga hadari ya taso, amma kuma ga babu wurin fakewa. Can sai ta hango wata yar bukka, ta ko nufi wurinta ta fake. Tana zaune a ciki, sai ta ga wata fitila ta kunna kanta da kanta, mamakin wannan ya kama ta, sai kuma ta ga cinya a gefe daya. Kafin ta gama mamaki sai kuma ta ga kai shi kadai a gefen cinya yana motsi. Sai cinya ta ce da ita: "Kai yana yi miki maraba."
Can kuma sai cinya ta yi nata motsin, sai kai ya ce da ita: “Cinya ma tana yi miki maraba da zuwa." Duka dai yarinya tana amsawa da cewa: "Na gode da wannan maraba." Suna nan zaune, sai kai ya yi wani motsi, sai cinya ta ce da yarinyar: "Wai yunwa yake ji; ki dauki wancan kwanon ki ba shi abinci." Ba tare da wani musu ba, 'Yar Mowa ta tashi ta zuba masa abinci, ta zauna kusa da shi da abincin a kan cinyarta har ya ci ya koshi. Sai ya sake yin wani motsin, sai cinya ta ce da yarinyar: "Wai ki ba shi ruwa." Nan da nan ta ba shi ruwa.
Suna zaune a haka, can sai ga wani wafcecen kumurci ya shigo, amma kuma ba ta ji tsoro ba. Jim kadan sai ta ga macijin ya fara aman kwaikwaye. Ya amayar da uku kanana, daga baya ya yi aman wasu manya uku. Da ya gama, sai cinya ta yi wani motsi, sai kai ya ce: "Wai idan gari ya waye za ki tafi, ki zabi kwaikwaye uku ki tafi da su, kuma kada ki fasa sai kin isa kusa da garinku."
Ta ce: "To. Na gode, Allah ya kai mu goben." Da gari ya waye, sai 'Yar Mowa ta tsuguna ta zabi kwaikwaye uku, amma kuma kanana ta zaba. Ta kama hanya tiryan-tiryan, ta doshi garinsu. "Kai yana yi miki maraba." Da ta isa bayan gari, sai ta fasa kwai daya, sai ta ga ingarman doki da adon kayan kawa da sauran kayan alatu iri-iri. Da ta fasa kwai na biyu kuma, sai ta ga 'yan mata goma suna dauke da kayan ado da kayan sawa iri-iri. Da ta fasa dayan, sai ga dukiya har da gida kerarre, da duk abin da za a nema don jin dadin duniya a ciki. Sai ta yi godiya ga Allah, ta taka ta hau dokin nan, ba ta zame ko'ina ba sai a kofar gidansu.
Da kishiyar uwar da 'Yar Bora suka gan ta da dukiya da kwalliya kamar sarauniya, sai kishiyar uwar ta nemi sanin yadda ta sami wannan abu haka. A nan ta ba ta labarin zuwanta Ruwan Bagaja, har zuwa inda ta fasa kwaikwayen nan guda uku. Sai uwar 'Yar Bora ta ce ita ma sai 'yarta ta je washe gari, ita ma ta samo nata.
Washe-gari tun da duku-dukun safiya, uwar 'Yar Bora ta tura ta wai don ta je ta wanke shimfida a Ruwan Bagaja. Ita kuwa ta kama hanya. Da ta je Ruwan Madara sai ta yi waka kamar yadda 'Yar Mowa ta yi. Sai ruwan ya ce, "Ni Ruwan Madara ne, ba Ruwan Bagaja ba. Amma in kina so, ki zauna ki sha." Sai ta ce: "To." A nan ta zauna, ta sha madara har sai da ta koshi. Ta tashi ta yi gaba, ko godiya ma ba ta yi ba. Da ta tarar da Rafin Shinkafa da Kaji, sai ta yi masa waka. Sai ya ce shi ba Ruwan Bagaja ba ne, Ruwan Shinkafa da Kaji ne; idan za ta ci, ta zauna ta ci. Sai 'Yar Bora ta ce: "Ai ko ba ka fada ba zan ci." Sai ta zauna ta ci har ta koshi. Ta sami ruwa ta kwankwada, ta yi gaba. Da ta isa Ruwan Jini sai ya ce shi ba Ruwan Bagaja ba ne, shi Ruwan Jini ne. In za ta sha to. Sai ta yi masa gatsine, ta bugi cinya irin yadda masu tsiwa kan yi, ta ce: "Me zan yi da wani ruwan jini?" Sai ta tofa masa yawu, ta wuce.
Da haka dai 'Yar Bora ta ci gaba har ta kai ga Ruwan Bagaja. Da ta tambaya ya ce shi ne Ruwan Bagaja, sai shi kuma ya tambaye ta abin da ya kai ta neman Ruwan Bagaja. Sai ta ce ta zo ne ta sami irin dukiyar da 'yar'uwarta ta samu a nan. Sai Ruwan Bagaja ya ce: "To ga shi kuwa yanzu dare ya fara yi." Kafin ma ya gama yi mata bayani sai hadari ya taso. Da ta hango wata bukka sai ta je ta shiga ta fake daga ruwan sama. Can sai fitila ta kunna kanta, sai ta ga cinya a gefe. Sai ta yi kururuwa, a gefe kuma sai ta ga kai ya ce da ita: "Kada ki ji tsoro."
Daga nan sai cinya ta yi motsi, sai kai ya ce: "Wai sannunki da zuwa." Da ta ji haka sai ta yi tsaki, irin wanda ta saba yi wa mutane, ta ce: "Mene ne kuma na wata cinya ta ce tana gaishe ni?" Da cinya ta ji haka sai ta yi motsi. Sai ta dubi yarinyar ta ce: "Kai ya ce wai ki ba shi abinci yana jin yunwa, ga abincin can ki dauko kici.
Da ta isa bayan gari, sai ta fasa kwai daya, sai ta ga ingarman doki da adon kayan kawa da sauran kayan alatu iri-iri. Da ta fasa kwai na biyu kuma, sai ta ga 'yan mata goma suna dauke da kayan ado da kayan sawa iri-iri. Da ta fasa dayan, sai ga dukiya har da gida kerarre, da duk abin da za a nema don jin dadin duniya a ciki. Sai ta yi godiya ga Allah, ta taka ta hau dokin nan, ba ta zame ko'ina ba sai a kofar gidansu.
Da kishiyar uwar da 'Yar Bora suka gan ta da dukiya da kwalliya kamar sarauniya, sai kishiyar uwar ta nemi sanin yadda ta sami wannan abu haka. A nan ta ba ta labarin zuwanta Ruwan Bagaja, har zuwa inda ta fasa kwaikwayen nan guda uku. Sai uwar 'Yar Bora ta ce ita ma sai 'yarta ta je washe gari, ita ma ta samo nata.
Washe-gari tun da duku-dukun safiya, uwar 'Yar Bora ta tura ta wai don ta je ta wanke shimfida a Ruwan Bagaja. Ita kuwa ta kama hanya. Da ta je Ruwan Madara sai ta yi waka kamar yadda 'Yar Mowa ta yi. Sai ruwan ya ce, "Ni Ruwan Madara ne, ba Ruwan Bagaja ba. Amma in kina so, ki zauna ki sha." Sai ta ce: "To." A nan ta zauna, ta sha madara har sai da ta koshi. Ta tashi ta yi gaba, ko godiya ma ba ta yi ba. Da ta tarar da Rafin Shinkafa da Kaji, sai ta yi masa waka. Sai ya ce shi ba Ruwan Bagaja ba ne, Ruwan Shinkafa da Kaji ne; idan za ta ci, ta zauna ta ci. Sai 'Yar Bora ta ce: "Ai ko ba ka fada ba zan ci." Sai ta zauna ta ci har ta koshi. Ta sami ruwa ta kwankwada, ta yi gaba. Da ta isa Ruwan Jini sai ya ce shi ba Ruwan Bagaja ba ne, shi Ruwan Jini ne. In za ta sha to. Sai ta yi masa gatsine, ta bugi cinya irin yadda masu tsiwa kan yi, ta ce: "Me zan yi da wani ruwan jini?" Sai ta tofa masa yawu, ta wuce.
Da haka dai 'Yar Bora ta ci gaba har ta kai ga Ruwan Bagaja. Da ta tambaya ya ce shi ne Ruwan Bagaja, sai shi kuma ya tambaye ta abin da ya kai ta neman Ruwan Bagaja. Sai ta ce ta zo ne ta sami irin dukiyar da 'yar'uwarta ta samu a nan. Sai Ruwan Bagaja ya ce: "To ga shi kuwa yanzu dare ya fara yi." Kafin ma ya gama yi mata bayani sai hadari ya taso. Da ta hango wata bukka sai ta je ta shiga ta fake daga ruwan sama. Can sai fitila ta kunna kanta, sai ta ga cinya a gefe. Sai ta yi kururuwa, a gefe kuma sai ta ga kai ya ce da ita: "Kada ki ji tsoro."
Daga nan sai cinya ta yi motsi, sai kai ya ce: "Wai sannunki da zuwa." Da ta ji haka sai ta yi tsaki, irin wanda ta saba yi wa mutane, ta ce: "Mene ne kuma na wata cinya ta ce tana gaishe ni?" Da cinya ta ji haka sai ta yi motsi. Sai ta dubi yarinyar ta ce: "Kai ya ce wai ki ba shi abinci yana jin yunwa, ga abincin can ki dauko ki ba shi."
A nan ma sai ta sake yin tsaki ta ce: "Kamar ni in ba shi abinci?" Sai ta tashi ta dauko abincin. Da ta ga kafafun kaji ne da kifi da naman rago da alkaki da nakiya, sai ta zauna ta cinye. Tana cin wannan abinci, sai cinya ta sake yin motsi. Shi kuma kai sai ya ce: "Wai ki ba shi ruwa."
Sai ta ce: "Amma fa cinyar nan da raini kike." Da ta dauko ruwan sai kai bai ci ba, kuma bai sha ba. Suna nan zaune, sai ga kumurci ya shigo, sai 'Yar Bora ta kwalla ihu. Macijin ya fara aman kwaikwaye shida. Uku manya, sauran ukun kuma kanana. Sai cinya ta yi motsi, sai kai ya ce: "Wai idan za ki tafi gobe ki debi kwai uku. In kin je bayan garinku sai ki fasa."
Da ta ji haka, sai ta karkace kai irin na marasa kunya ta ce: "Yau ni wani abu za ku gaya mini in diba? Ai ko ba ku fada ba zan diba."
Da gari ya waye, sai ta debi kwaikwaye uku amma manya, ta tafi. Da ta fara 'yar tafiya sai ta ce: "Yanzu wai har ma sai na je gida zan fasa kayan nan?" Sai kawai ta fasa kwai biyu tare. Tana fasawa sai ga jakai da kutare da kudaje suna bin ta. Sai ta fasa na uku, sai ga tarkacen shara da tsummokara tili-tili. Sai kutaren nan suka dora ta a kan jaki, suna raka ta. Kudaje na bin su har gida.
Da uwar ta ga 'yarta, sai ta gudu. Da 'yar ta ga uwarta na gudun ta, sai ta ce da ita: "Tsaya mana, ni ce 'yarki fa."
Sai uwar ta ce: "A'a, yau na rabu da ke, ba ni ba ce." Sai ta gudu ta bar ta da kutarenta da jakan nan da kudaje suna ta zaga gari. Mutanen kauyukan kusa da su da suka ji labari suka yi ta tururuwa suna zuwa kallo.
Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
1. Yi wa yara kyakkyawar tarbiya shi ne babban jarin da za su juya don samun kyakkyawar rayuwa.
2. Rashin tarbiya mai kyau shi ne jigon kaiwa ga rashin nasara.
3. Kwadayi mabudin wahala.
Tushe: Mun ciro wannan labarin daga littafin *Taskar Tatsuniyoyi* na Dakta Bukar Usman.