Harin 'Yan Bindiga Ya Sanya Garin Maidabino Cikin Tsoro Da Matsanancin Hali
- Katsina City News
- 25 Jun, 2024
- 329
Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times. 25, 6, 2024
Tun bayan mummunan ta'addancin da barayi masu satar mutane don neman kudin fansa suka kai a garin Maidabino na ƙaramar hukumar Danmusa a jihar Katsina, a ranar Asabar 23 ga watan Yuni, al'ummar garin suka shiga mawuyacin hali na kunci, yunwa da rashin tabbas.
'Yan ta'addan da suka shiga garin da yammacin ranar Asabar, sun kwashe fiye da awa shida suna ta'addanci ba tare da wani ɗauki ko taimakon jami'an tsaro ba, inda suka ƙone gidaje da shagunan sayar da kayan masarufi, tare da kashe mutane 9 da sace mata da kananan yara da ake kyautata zaton sun kai dari. A lokaci guda kuma suka kwashe dukiya mai yawan gaske suka shiga da ita daji.
Sun fasa sito-sito na abinci wanda suka ɗebo wasu, wasu kuma suka banka masa wuta. Hatta dakunan saida magani (chemist) basu bari ba. Haka zalika sun ƙona buhunnan takin zamani wanda al'ummar garin suka tanada don aikin gona. Sun ƙona gidan sakataren ƙaramar hukumar Danmusa tare da duk abin da ke cikin gidan, sannan suka bi cikin unguwanni suna ƙona gidaje.
Bayan awa arba'in da takwas da wannan mummunan ta'addanci, mutanen garin Maidabino sun shaida wa jaridun Katsina Times irin mawuyacin halin da suke ciki na kuncin rayuwa. Babu abinci babu magunguna, sun ce abincin da zasu saya ma su sarrafa su ci, an ƙone shaguna basu san inda zasu je su sayi abinci ba. Sannan kuma basa iya fita daga garin zuwa inda harin bai shafa ba don su sayi kayan abinci. Yunwa zata iya kamasu a wannan halin, inji wani mazaunin garin.
Sun ce basu iya fita daga garin sai da rakiyar jami'an tsaro, amma kuma babu su balle su raka su. Ana cikin wannan halin da yammacin ranar Litinin kuma sai 'yan ta'addan suka dawo, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi. Amma a wannan lokacin jami'an sojoji sun kawo masu ɗauki inda suka yi nasarar kora su. Abinda bamu tabbatar ba a wannan lokacin shine kamawa ko kashewa daga ɓangaren Al'umma ko 'yan ta'addan, kasancewar masu bamu rahotannin suna ɓoye ne basu iya tantance yanayin ta'addancin ba.
Jihar Katsina da jihohin Arewa maso yammacin Najeriya suna fama da rikicin 'yan bindiga masu garkuwa da mutane, wanda yaki ci yaki cinyewa. Dalilin wannan mummunar matsala yasa kungiyar gwamnonin Arewa maso yamma da gwamnatin tarayya haɗin gwiwa da UNDP daga Majalisar Dinkin Duniya tare da wakilan su, suka shirya wani gagarumin taro na kwana biyu akan tsaro da yanda za'a iya shawo kansa. Musamman a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi da Kaduna.
Taron da aka fara a ranar Litinin wanda mataimakin shugaban kasar Najeriya, Mr. Kashim Shettima ya buɗe a madadin shugaban ƙasa Mr. Bola Ahmed Tinubu, ya haɗa dukkanin bangarorin tsaro a Najeriya inda ake tattauna hanyoyin da za a tunkari matsalar don shawo kanta. Ana gudanar da taron a garin Katsina, babbar fadar gwamnati jihar Katsina bisa jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnoni bakwai na Arewa maso yamma, Malam Dikko Umar Radda na jihar Katsina.