Sharhin Jaridun Katsina Times: ZAMAN SHUGABANNIN KANANAN HUKUMOMIN KATSINA A OFIS HARAMTACCE NE: BISA DOKA
- Katsina City News
- 18 Apr, 2024
- 721
@ www.katsinatimes.com
Jaridun Katsina Times da Taskar Labarai da ke da mazauninsu a birnin Katsina, kuma suke yaduwa a duk fadin kasar nan, na kira ga gwamnan Katsina, Dakta Dikko Umar Radda da ya yi gaggawar shelanta sauke shugabannin kananan hukumomin jihar Katsina bisa dalilai kamar haka:-
Jaridun sun samu kwafin dokoki na iyakar tsawon lokacin da shugabannin za su yi a kan mulki in an zabe su.
Dokar da aka yi ta shekarar 2018 ta ce, shugabannin za su yi shekaru uku ne kafin su sauka a sake zabe.
Amma dokar da majalisar dokokin jihar Katsina ta yi a shekarar 2023, kuma gwamnan Katsina na lokacin ya saka mata hannu aka kuma buga ta madabbar gwamnatin Katsina a matsayin doka, ya ce, duk ciyamomin da aka zaba, za su rike mukaminsu a tsawon shekaru biyu ne.
Mutanen Katsina a shekarar 2022 sun je akwatin zabe sun jefa kuri'a ne a matsayin za su zabi shugabannin da za su yi shekaru biyu.
An rantsar da wadannan shugabannin a gaban dubban jama'a, kuma Babban Jojin jiha ya rantsar da su a ranar 14 ga Afrilu 2022. a matsayin za su yi shekaru biyu.
A wannan doka suka sanya hannu, bayan an rantsar dasu .da kuma wannan doka ,Babban jojin jiha ya dogara ya rantsar dasu.
Wadannan shekara biyu sun kare a ranar 14 ga watan Afrilu, 2024.Dokar da ta ba su shekaru biyu babu wuri ko lokacin aka canza mata fasali.
Wannan ya nuna duk kwana daya bayan 14 ga watan afrilu 2024. na wadannan shugabannin kananan hukumomin a bisa kujerarsu haramtacce ne. Duk wani aiki da za su yi da sunan matsayinsu ya haramta.
Abin da ya kamata ga gwamnatin Katsina ta yi shi ne, ko dai ta shelanta mayar da su kantomomi, ko kuma ta sauke su.
Wannan yana da kyau tun da wuri, tun kafin wata kungiya, ko jam'iyya ko wasu mutane su kai gwamnatin ta Katsina kara a gaban kotu, wanda hakan zai zama bata lokaci da barnar kudin al'umma na muhawara a kotu.