TARIHIN MARIGAYI ALH. MAMMAN BUTAKA DANDANI. 1909- 2003

top-news


Marigayi Alh. Mamman Buta Kadandani Bafullatanine, an haifeshi shekarar ta 1909 agarin Kadandani, Karamar Hukumar Rimi, ya rasu a shekarar ta 2003, yana da shekara 94 a Duniya, yabar yaya da jikoki. 

Marigayi Alh. Mamman Buta babban dan Kasuwane, manomi, yana Kiyo, dan siyasa, Noman dayake yi kaf agarin Kadandani babu maiyin kamarsa alokacin, Mota yasa domin ta rinka dauko masa kayan gona dana sauran al'ummar gari a kyauta saboda ya kara masu kwarin gwiwa, mafi yawa gyadar da'ake nomawa shike sayen ta, saboda tana masu wahalar saidawa alokacin. A siyasa, Marigayi Alh. Mamman Buta yayi Kansila mai wakiltar Gundumar Rimi a shekarar ta 1976, 1st Oktoba, sannan Katsina tana karkashin Jahar Kaduna, yayi Kansilan tsakanin mulkin Janar Murtala. Kansilan dayayi da farko nadasu akayi, daga bayane yazo ya tsaya takarar Kansila, yayi nasarar cin zabe, sannan babu wata jam'iyya, daya daga cikin wanda sukayi siyasa tare shine Marigayi Sen. Abba Ali (Turakin Katsina) shine Civaman na Karamar Hukumar Katsina, a shekarar ta 1976- 1979 An zabe shi Kamsila on non party basis kuma an kaddamar dasu 1st December, 1983 October, 1976 har zuwa juyin mulkin 31st

Marigayi Alh. Mamman Buta mutunne mai kishi da san cigaba dabaya jin kyashin ya sadaukar da dukiyarsa ga al'umma, rumbun hatsi yake budewa yana rabama al'umma, idan ya fita cikin gari wajan gaishe gaishe, dayaga mabukaci na neman taimako zai tsaya yace abashi abinda yake bukata, sannan yayi kokarin wajan ganin cewa ya samar da titi saboda manoma su samu saukin fitowa da kayan gonarsu, hakan bai samu ba amman har yanzu Kwalbati nanan dayayi kafin ashigo cikin garin Kadandani saboda ya dauki taimako mahimmanci. kafin ya rasu ya barma iyalansa wasiyya ta taimakon al'umma, yace duk wanda ya samu dukiya, yayi kokari ya taimaki al'umma, yace duk wanda yake taimako, arzikinsa gaba yakeyi, ba baya ba, yace duk arzikin da ba'a taimakon Al'umma dashi, ba arziki bane. Daga cikin iyalansa Alh. Mamman Buta, Alh. Salisu Continental Computers ya dauki wasiyyar da Mahaifinsu ya bari, a fuska shike kama da Mahaifinsu, shiya gaje taimakonsa, yanzu taimakon da yake yi, ba Karamar Hukumar Rimi kadai ya tsaya ba, har a wasu kananun hukumomi ya leka, yanzu cikin mazabun da muke dasu 361 a jahar
Katsina akwai masu dogaro da kansu ta dalilinsa.Titin da Alh. Mamman Buta yaso ya samar. hakan bai yiwu ba, titin saidai Alh. Salisu Continental ya samar dashi.
Marigayi Alh. Mamman Buta mutum ne wanda ya inganta tare da kyautata dangantaka tsakanin shi da malaman addini, wannan ya bashi dama ta yima addinin muslunci hidima mai dunbun yawa.
Inganta hanyar shiga Kadandani daga Eka inda ake zubin kasa da yin kwalbatoci da kula dasu. Shi yayi jagorancin kafa sababin kasuwanni da bude santoci na Sabon layi, Are, Jikanshi, Ladanawa. Ya jagoranci gina Dam dake kwanar Are domin samar da ruwan sha da kuma noman rani lokacin gwamnatin Kaduna State.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *