Jigon dan siyasa, dan kasuwa, kuma kwamishinan Muhalli na jihar Katsina, Hon. Hamza Sule Faskari, ya yi bikini Sallah tare da al'umarsa a garin Faskari inda ya amshi gaisuwa Barka da Sallah daga kungoyin daban daban.
Hamza Sule wanda shine Wamban Faskari kuma Sadaukin Kasar Hausa, ya amshi bakuncin kungiyoyin ‘yan siyasa, da matasa, da marasa galihu, da kungiyoyin ci gaban al’umma a gidansa da ke Faskari, ya kuma sada zumunci da ‘yan uwa da abokan arziki.
Kamar yadda ya saba, Hon. Hamza Sule ya yi ma bakin nasa liyafar cin abinci game da basu goron Sallah, game da jagorantar gudanar da addu'o'i ga jiha da kasa bakidaya.
Kowace mazaba a Karamar Hukumar Faskari ta samu Naira 500,000 yayin da mazabu uku suka samu karin Naira 200,000 domin la'akari da yawan wadanda suka kawo masa ziyara daga mazabun, inda jimillar kudin ya kai Naira 5,600,000.
Hakazalika kungoyin 'yan siyasa guda biyar sun samu jimillar Naira 2,500,000 inda kowace kungiya ta samu Naira 500,000 domin kara musu kwarin gwiwa a aiyukan da suke yi.
Kungiyoyin sune Wambai Support Organisation Funtua Zone, Wambai Mataki na Gaba Funtua Zone, Wambai Political Awareness Funtua Zone, 11 Thousand for Wamban Faskari Funtua Zone, da Wambai House to House Funtua Zone.
Tawagar kungiyoyi daban-daban daga karamar hukumar Sabuwa suma sun samu Naira miliyan uku yayin da wata kungiya daga karamar hukumar Dandume ta samu Naira 500,000 a matsayin goron Sallah.
Hon. Hamza Sule ya kuma yi amfani da bikin Sallar wajen tallafa wa marasa galihu da kungiyoyi daban-daban, cikinsu har da wasu mutanen daga Dogon Awo da aka ba Naira N500,000 domin kai wani mara lafiya asibiti da kuma wata mata da aka bata Naira 200 domin ta kai 'yarta asibiti.
Hon. Hamza Sule ya kuma jagoranci addu'o'i na musamman domin samun karin nasara ga gwamnatin Malam Dikko Umar Radda da gwamnatin jam’iyyar APC a dukkan matakai.
Sun kuma gudanar da addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a yankin Funtua da daukacin jihar Katsina.
/////////////