AFAN Ta Taya Al'ummar Musulmi Murnar Shiga Sabuwar Shekarar 1446AH A Katsina
- Katsina City News
- 08 Jul, 2024
- 339
Kungiyar manoma ta ƙasa reshen jihar Katsina AFAN ta taya al'ummar musulmi shiga sabuwar shekarar musulunci ta 1446AH
Bayanin haka na kunshe a cikin wata sanarwa wanda shugaban kungiyar Hon. Ya'u Umar Gwajo-gwajo ya sanya hannu aka rabawa manema labarai a Katsina
Shugaban kungiyar ya yabawa gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa bisa ayyana ranar 1/1/1446AH a matsayin ranar hotu a jihar ta Katsina.
Saboda haka ne ya yi kira ga al'umma musamman ma'aikatan gwamnati da na kamfanoni da su yi amfani da wannan lokaci wajen sanya jihar Katsina cikin addu'o'in samun zaman lafiya.
Kazalika ya nuna jin dadin sa akan yadda gwamnatin jihar Katsina ta fara rabon takin zamani ga manoma domin amfani da shi a wannan damina.
Hon. Ya'u Umar Gwajo-gwajo ya ja kunnen manoma waɗanda suka amfani da takin zamani da su yi amfani da shi yadda ya da ce, ba wai su sayar ba, wanda ya ce yin amfani da shi zai iya samar da abinci mai yawa da ka iya rage tsadar shi da ake fuskanta a Nijeriya.
"A kodayaushe zamu goshe ba, sai mun jinjinawa Malan Dikko Umar Raɗɗa bisa ƙoƙarin da ya yi na ɗaukar ma'aikatan gona 722 domin su koyar da manoma dibarun aikin gona na zamani kuma alama ta nuna hakan zai haifar da ɗa mai ido" inji shi
.
A ƙarshen shugaban kungiyar ya ƙara nuna buƙatar da ake da ita ga al'umma da su cigaba da rokon Allah ruwan sama mai albarka musamman da yanzu an kawo tsakiyar damina kuma babu ruwan sama wanda yana iya shafar shukar da aka yi