Yan bindiga sun sace daliban furamare sama da 200 a jihar Kaduna
- Katsina City News
- 07 Mar, 2024
- 1042
An sace ɗaliban firamare da na sakandare kusan su 200 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.
Lamarin ya faru ne da safiyar yau (Alhamis) lokacin da ɗaliban ke taro (assembly) da misalin karfe takwas da rabi.
Wani babban jami'in gwamnatin jihar Kaduna ya tabbatar wa BBC afkuwar lamarin amma ya ce ya zuwa yanzu babu cikakken bayani kan lamarin.
Wani da ya shaida faruwar lamarin ya ce "yau da misalain ƙarfe 8:30 an gama asambili ke nan sai ga shigowar waɗannan mutane (ƴan fashi) daga kowane ɓangare, suka zo suka yi wa makarantar ƙawanya suka kwashi ɗalibai na firamare da sakandare kusan 200 suka wuce da su, har da malami ɗaya na sakandare".
Shaidan ya kuma bayyana wa BBC cewar maharan sun harbi yaro ɗaya wanda aka garzaya da shi asibitin da ke garin Birnin Gwari.
Yaran da lamarin ya rusta da su, kamar yadda shaidan ya tabbatar wa BBC shekarunsu sun kama ne daga takwas zuwa 15.
Ko a watan Janairun shekarar nan, wasu ƴan bindiga sun shiga ƙauyen na Kuriga, inda suka kashe shugaban makaranta tare da sace matarsa.
Kuriga ƙauye ne da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, yankin da ya yi ƙaurin suna wajen ayyukan ƴan fashin daji.
A shekarar 2023 ƴan bindiga sun kai hari kan sojojin da ke sintiri a kan hanyar tare da ƙona mota mai sulke.
Sace-sacen ɗalibai irin wannan na tuno wa al'ummar Najeriya da satar ƴanmatan makarantar sakandaren Chibok da ke jihar Borno, inda a daren 15 ga watan Afrilun 2014 mayaƙan Boko Haram suka kai farmaki a makarantar tare da sace ɗalibai sama da 200