Taron A Kan Waƙoƙin Rarara: KWALEJIN PLBC ZA SU KAI JAMI'AR FUDMA KOTU

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12072025_123421_FB_IMG_1752145744815.jpg

Mu'azu Hassan  @ Katsina Times 
 
A wata takarda da Hukumar Kwalejin PLBC suka raba wa manema labarai, sun bai wa Jami'ar Tarayya da ke Dutsinma awa 48 da su janye kalamansu na cewa ba su san da maganar taron ƙara wa juna sani da Kwalejin ta shirya tare da Jami'ar ba a kan Rarara da waƙoƙinsa, ko kuma su maka su a kotu.

Takardar da Usman Umar, wanda yake shi ne mai magana da yawun Kwalejin, kuma Sakatarenta ya sanya wa hannu a ranar Juma'a 11/7/2025.

Takardar manema labaran ta ce, sanarwa ta Jami'ar FUDMA ta ɓata masu suna, kuma ta jawo masu cece-kucen da ba za su iya ƙyalewa ba alhali suna da gaskiyarsu.

Takardar ta ce a shekarar 2016 aka kafa PLBC, kuma zuwa yanzu 2025 sun kashe sama da Naira biliyan ɗaya don ilmantarwa da wayar da kan al'ummar. 

Takardar ta ƙara da cewa sama da mutane dubu 300 suka amfana da su, yayin da sama da mutane 1000 na samun horo a wurare daban-daban a ƙarƙashin kulawar PLBC.

Suka ce a baya sun shirya taron ƙara wa juna sani a kan Marigayi Umaru Musa 'Yar'adua da MD Yusuf a kan tsaro da a kan matan Hausawa da Mamman Shata.

Suka ce taron ƙara wa juna sani a kan waƙoƙin Rarara, Kwalejin ta fara maganarsa ne tun a shekarar 2024.

Takardar ta ce, manyan Malaman Jami'ar daga ciki da wajen Katsina ke cikin Kwamitin PLBC na shirya wannan taron na Rarara.

Takardar ta ce, kuma Kwamitin ya rubuta wa Jami'ar a rubuce yana son su yi haɗin gwiwa wajen shirya taron, kuma malamai uku da Jami'ar FUDMA suna a cikin Kwamitin taron. Malaman sune Farfesa Bashir Aliyu Sallau. Dr. Ibrahim Adamu Malumfashi, Dr. Yahya Abbas. Waɗannan ukun Jami'ar ta karɓe su a matsayin wakilanta a shirya taron kamar yadda suka tabbatar mana.

A takardar sun kawo wani saƙo da aka turo ta WhatsApp cewa Jami'ar ta amince za ta haɗa kai da PLBC wajen shirya taron.

Takardar ta ce, tattaunawa ta ci gaba tsakanin Kwamitin shirye taron har da wakili daga Jami'ar FUDMA a ranakun 29 ga Yuni zuwa 6 ga Yuli, inda aka fitar da tsarin taron da ranar da za a yi taron, aka kuma kafa kwamitoci waɗanda dukkaninsu malaman Jami'a ne ke jagorantar su.

Takardar ta ce duk da Jami'ar FUDMA ta ce ba ta san da taron ba, cin fuska ne da ɓatanci ga PLBC.

Don haka PLBC ta bai wa Jami'ar awa 48 da ta janye kalamanta ta kuma ba da haƙuri a kuma buga a jaridun DAILY TRUST, GUARDIAN, KATSINA TIMES, KATSINA POST, MOBILE MEDIA CREW, in kuma ba haka ba, cikin awa 48 za su tafi kotu.

Takardar ta yi kira ga masana da sauran al'umma su ba su haɗin kai wajen shirya wannan taron domin ƙara wa juna sani da kuma ilmi wanda shi ilmi ba shi da katanga.

Follow Us