Daga Auwal Isah, Katsina Time
A yayin da Jami’ar Sufuri ta Tarayya da ke Daura a jihar Katsina ke cika shekaru biyu da kafuwa, jami’ar ta bayyana wasu muhimman nasarori da kuma matsalolin da ta ke fuskanta, tare da samun babban tallafi daga Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) wadda ta mika mata katafaren ginin cibiyar fasahar sadarwa.
Shugaban jami’ar, Farfesa Umar Adamu Katsayal, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata, 20 ga Mayu 2025 a Daura. Ya ce tun kafuwar jami’ar a shekara ta 2023, an fara gudanar da karatu nan take, wani abin alfahari da ya bambanta jami’ar da sauran sabbin cibiyoyin Ilimi a fadin ƙasar.
Daga cikin nasarorin da jami’ar ta samu har zuwa yanzu akwai kulla haɗin gwiwa da jami’o’i da cibiyoyin bincike na gida da na ƙasashen waje, irin su Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Cibiyar Nazarin Sufuri ta Ƙasa (NITT), Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), da Jami’ar Sufuri ta Rasha. Haka kuma tana da hulɗa da hukumomin sufuri kamar Shippers Council, NIMASA da Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA).
Baya ga haka, an haɗa jami’ar cikin jerin cibiyoyin da za su ci gajiyar tallafin TETFUND domin inganta kayan aiki da horas da ma’aikata, kamar yadda Farfesa Katsayal ya bayyana.
Sai dai ya ce jami’ar na fuskantar manyan ƙalubale, musamman karancin kudaden gudanarwa da suka shafi tsaro, gyaran dakunan kwana da karatu da kuma samar da kayan aikin jarrabawa. Haka kuma, rashin haɗa jami’ar da layin wutar lantarki na ƙasa na daga cikin matsalolin da ke hana sauƙin gudanar da aiki, inda jami’ar ke dogara da injinan dizel da wuta mai aiki da hasken rana (inverters) domin samar da hasken wuta.
Duk da haka, Farfesa Katsayal ya bayyana cewa jami’ar ta gina wani dogon tsarin ci gaba na shekaru 15 da za a aiwatar a matakai uku na shekaru 5-5-5 domin tabbatar da ingantacciyar cibiyar ilimi da bincike.
A wata gagarumar nasara da ta kara ƙarfafa ci gaban jami’ar, Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta mika katafaren ginin cibiyar fasahar sadarwa (ICT Park) ga jami’ar, wanda ya ƙunshi dakin taro mai kujeru 100, dakunan koyar da fasaha guda biyar, wurin hutawa mai kujeru 24 da kwamfutoci masu inganci, da dakunan kirkire-kirkire na zamani.
Shugaban NCC, Dr. Aminu Maida, wanda ya kaddamar da cibiyar, ya ce wannan aiki na daga cikin shirin gwamnatin tarayya na tallafa wa fasahar zamani da bunkasa tattalin arzikin dijital. Ya bayyana cewa cibiyar za ta bai wa daliban jami’ar damar karatu da bincike a fannonin injiniyan jiragen kasa, dabarun sufuri da fasahar jigila tare da sabbin dabaru irin su Artificial Intelligence (AI) da Internet of Things (IoT).
Shugaban jami’ar, Farfesa Katsayal, ya gode wa hukumar NCC bisa wannan gudummawa tare da bayyana cewa jami’ar za ta tabbatar da ingantaccen amfani da cibiyar don amfanin dalibai da al’ummar jihar Katsina baki ɗaya.
Wannan ci gaba ya yi daidai da manufofin gwamnatin tarayya na tattalin arzikin fasahar zamani dijital da kuma hangen nesa na Ministan Sadarwa da Kirkire-Kirkire, Dr. Bosun Tijani, na tabbatar da cewa Najeriya ta zama jagora a fannin fasahar dijital a nahiyar Afrika.
A yayin da jami’ar ke cika shekaru biyu, ci gaban da aka samu ya nuna alkiblar gina cikakkiyar cibiyar ilimi ta sufuri a Najeriya, muddin aka ci gaba da magance ƙalubalen da ta ke fuskanta.