Haihuwar Farashi: Gidajen Burodi Kashi 55% a Jihar Katsina sun rufe - Abdulkadir Abdullahi, Alliance Bread

top-news



Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

Fiye da rabin gidajen burodi a jihar Katsina sun rufe saboda matsalolin tattalin arziki, in ji Alhaji Abdulkadir Abdullahi, Manajan Darakta na Kamfanin Alliance Bread. Ya ce, daga cikin kashi 100, kaso 55 sun rufe, yayin da kaso 25 ke asara, sai kuma kaso 20 kadai ke maida kudi.

A wata hira da ya yi da Katsina Times ranar Lahadi a ofishinsa dake titin Yahya Madaki, cikin birnin Katsina, Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan masarufi da saukar darajar naira sun jefa masana'antu cikin mawuyacin hali. 

"Abin da ke daure kai shi ne yadda kayan da muke siyo daga waje ke kara tsada duk da cewa darajar naira ta sauka," in ji shi. Ya kara da cewa babu wani abu da ake amfani da shi wajen hada burodi a Najeriya, "hatta yeast daga China muke siyo shi."

Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa rufe gidajen burodi a jihar Katsina ya haifar da karuwar rashin aikin yi da kashi 55 cikin dari. Ya ce, "Jihohin Arewa da Najeriya baki daya na fama da wannan matsalar, ba tare da wani yankin da ya tsira ba. Wannan na nuna yadda masana'antu ke rugujewa da kuma karuwar rashin aikin yi ga matasa."

A karshe, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Katsina da su taimaka wajen rage tsadar burodi wanda ya zama abincin talakawa. Ya kuma gode wa gwamnatin jihar bisa tallafin da take ba masu kananan sana'o'i, tare da yin kira da a ware kaso mafi tsoka na kudaden tallafi don bunkasa sana'ar burodi.