Daga Auwal Isah Musa.
Gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar kaddamar da shirye-shiryen aikin Hajjin bana (2025) a jihar.
Bikin kaddamarwar wanda aka gudanar da shi a sansanin Alhazan jihar na Katsina, ya samu halartar manyan Malamai, 'yansiyasa da masu ruwa da tsaki a harkar aikin Hajji.
Tun farko da yake jawabi a yayin kaddamar da tashin Alhazan, Gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Honorabul Faruq Lawal Jobe, ya ja hankalin maniyyatan da cewar su kasance wakilai na gari ga jihar da ma kasa baki daya, "Ku nuna halaye na kwarai a wannan tafiya mai muhimmanci zuwa kasa mai tsarki".
"Wannan tafiya Ibada ce. Tafiya ce ba ta kashin kanku kawai ba; ku wakilai ne na Jihar Katsina da Nijeriya baki daya." Ya an karar da su.
"Allah ya karbi Hajjinku, ya kuma dawo da ku lafiya." Ya yi masu addu'a.
Jobe, ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta tura jami'ai 175 zuwa Saudiyya, ciki har da Likitoci, Malamai da ma’aikatan hukumar jin dadin alhazai domin jagoranci da kula da mahajjata.
Hakazalika, Jobe, ya bayyana wa maniyyatan cewar gwamnatin jihar karkashin Malam Dikko Radda ta kuma biya masu kudin hadaya ( yanka) ga daukacin maniyyatan su 2047, na kimanin Riyal 600 na kudin Saudiyya ga kowanensu.
Daga karshe, mataimakin gwamnan ya kuma gargadi maniyyatan da cewar su yi kaffa-kaffa da kula da guzurinsu, "Ku nisanci hadurra tare da amfani da cibiyoyin musayar kuɗi da aka amince da su kawai a Makkah da Madinah." Ya nunasshe su.
Shi ko a nasa jawabin, shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina, Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama, ya tabbatar wa maniyyatan cewar gwamnatin ta kammala dukkan shirye-shirye domin tabbatar da tafiya cikin kwanciyar hankali.
"Ko da yake ana fuskantar kalubale na tattalin arziki, amma gwamnati ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da cewa mahajjatan Katsina za su gudanar da aikin Hajji cikin mutunci da sauki," in ji shi.
Shugaba hukumar alhazan jihar, Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai, shi ma a nashi jawabin ya ja hankalin maniyyatan musamman kan yin biyayya ga shugabanninsu, zama da al'umma lafiya da kuma maida hankali kan ibada.
"Haƙuri, tawali’u da biyayya su ne sirrin samun Hajjin karbabba. Ku nisanci rigima da abin da ba dole ba," ya Nasihance su.
Bikin kaddamawar tashin Alhazan ya samu halartar Malamai da suka hada da: Dr. Aminu Abdullahi Yammawa, Malam Bin Usman Kano da kwamishinan hukumar Hajji ta kasa mai kula da yankin Arewa maso Yamma.
Sauran sun hada da: Danmajalisar tarayya mai wakiltar Kaita/Jibia, Hon. Sada Soli Jibia, Kakakin majalisar dokokin jihar Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, babban alkalin jihar Justice Musa Danladi Abubakar, babban Khadi Dr. Kabir Mustapha, 'yanmajalisar dokokin jihar; mambobin majalisar zartarwa da sauran manyan jami'an gwamnati.
Bugu da kari, fuk a wajen bikin kaddamar da tashin Alhazan, an kuma hada da kaddamar da sabon littafi kan Hajji da Umrah, wanda kungiyar Gwagware Foundation ta wallafa, wanda aka sadaukar da shi ga marigayiya Hajiya Safara'u, mahaifiyar Gwamna Radda.