Malaman Firamare na Katsina Sun Koka Kan Kwangilar Kwamfuta da ta Ci Dubu Uku-uku a Albashin su
- Katsina City News
- 11 Jul, 2024
- 794
Katsina Times 11,7,2024
Jaridar Katsina Times ta samu korafi daga Malaman makarantun firamare na jihar Katsina bisa cire masu naira dubu uku kai tsaye daga albashin su na watan Yuni da ya gabata.
Malaman sun koka cewa an sanar da su cewa kudin da aka cire za a yi amfani da shi ne wajen koya masu yadda ake sarrafa kwamfuta. Sun bayyana cewa an tara wasu malamai kaɗan, aka kunna masu kwamfuta na awa daya da rabi, sannan aka ce an kammala horon kuma an ci dubu ukun su.
Malaman sun ce, daga abin da suka ji daga wadanda suka halarci horon, babu wani ilimin da za a iya samu daga wannan horo. Sun kara da cewa mafi yawan kwamfutocin basu aiki, an zaunar da su kawai aka ce su tafi an kammala horon.
Malaman sun ce abin da aka yi masu da naira dubu uku yafi kama da wasan yara da aka bar yayin shi shekaru ashirin da suka wuce. Sun kuma zargi cewa ba a nemi ra’ayinsu ba na ko suna bukatar horaswar ko a’a, balle neman yancinsu kafin a cire masu kudin a cikin albashin su.
Malaman sun zargi shugaban hukumar makarantun firamare na jihar Katsina da kasa kawo ma hukumar kowace irin cigaba tun da ya hau bisa kujerar. Binciken Katsina Times ya gano cewa wani kamfani mai zaman kansa aka baiwa wannan makudan miliyoyin kudade don horas da malaman makarantun firamare.
Sai dai binciken ya nuna cewa horon yana da tasgaro a cikin shi, kuma aikin bai ci darajar kudin da aka cire ga malaman ba. Wannan horaswa ba zata taimaki malaman ko ya inganta koyarwar da suke ba.
Mun tuntubi mai magana da yawun hukumar malaman makarantun firamare, Alhaji Badaru Jikamshi, inda ya sheda mana cewa sun samu labarin wadannan korafe-korafen, kuma sun gayyaci shugaban kula da bada horon domin tattaunawa da shi, kuma zasu fitar da matsaya akan batun.