Wakilan IPI Sun Ziyarci Ministan Yaɗa Labarai Na Najeriya

top-news

Katsina Times 

Wakilan cibiyar yan jaridun nan ta kasa da kasa, reshen Najeriya, mai suna "international press institute" ( IPI) ta kaiwa ministan watsa labarai da gyaran akida na kasa ziyarar ban girma.Alhaji Muhammed Idris 

Wakilan bisa jagorancin shugaban cibiyar reshen Najeriya, Babban editan jaridar premium times miskiliu Mojed. da sakataren ta Ahmed I shekarau daga kamfanin rukunin jaridun Daily trust.da sauransu.cikin wakilan da cibiyar ta zaba don ziyarar harda Muhammad Danjuma mawallafin jaridun Katsina Times da jaridar Taskar.

Shugaban cibiyar reshen Najeriya, ya bayyana ma Ministan ayyukan cibiyar wadanda suke tabbatar da yancin yan jaridu don yi aikin su da gaskiya kuma da zuciya daya.
Ya bayyana cewa cibiyar an kafa ta a kasar Austria a shekarar 1950,shekaru  73 da suka gabata, kuma tana da rassa a duk kasashen yan duniya.

Shugaban ya bayyana cewa, kaidojin zama memba a duniya suna da sharudda masu tsauri wannan ya sanya membobin ta cikakkun yan jaridu wadanda suka San aikin.
A Bangaren ministan  ya jaddada goyon bayan shi ga cibiyar da tabbatar da aiki tare.