Daga Katsina Times
Hukumar Kula da Hanyoyin Sufuri ta Jihar Katsina (KASSAROTA) ta bayyana damuwa tare da ba da haƙuri ga al’ummar jihar bisa wani lamari da ya faru tsakanin wasu jami’anta da wani matashi mai suna Aminu Abdulhamid.
A cewar wata sanarwa da Hukumar ta fitar, lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026. KASSAROTA ta jaddada cewa abin da ya faru bai yi daidai da ƙa’idojin aikinta da manufofin Gwamnatin Jihar Katsina ba, musamman waɗanda suka shafi kare rayuka, dukiya da kuma tabbatar da bin dokokin hanya.
Hukumar ta bayyana cewa wanda abin ya shafa, Malam Aminu Abdulhamid, ya halarci ofishinta da kansa a ranar 27 ga Janairu, 2026, inda ya ba da haƙuri tare da amincewa cewa wasu daga cikin ayyukansa sun taimaka wajen faruwar lamarin.
Sai dai duk da hakan, KASSAROTA ta sanar da kaddamar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya faru. Hukumar ta kuma tabbatar da cewa za a ɗauki matakan ladabtarwa kan duk wani jami’i da bincike ya tabbatar ya aikata abin da ya saɓa da doka ko ƙa’idojin aiki.
Haka kuma, KASSAROTA ta ba da tabbacin cewa za ta tabbatar da adalci, tare da ƙara horaswa da tsauraran matakan sa ido domin inganta ayyukan jami’anta da kauce wa faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
Sanarwar ta fito ne dauke da sa hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Abubakar Marwana Kofar Sauri.