Yan bindiga sun. Dora wa Al'umma Haraji, Ana Kuma Cin Zarafin Matansu — Wasu Mazauna Jihar Neja

Daga Mu'azu Hassan  @ Katsina TimesJaridar Weekend Trust ta ranar Asabar, 25 ga Yuli, 2026, ta wallafa rahoto kan yadda 'yan bindiga ke gallaza wa al'ummomin wasu yankuna a Jihar Neja,…

Katsina City News July 25, 2026  ·  12:00 AM
| 26 Views
Yan bindiga sun. Dora wa Al'umma Haraji, Ana Kuma Cin Zarafin Matansu — Wasu Mazauna Jihar Neja
Yan bindiga sun. Dora wa Al'umma Haraji, Ana Kuma Cin Zarafin Matansu — Wasu Mazauna Jihar Neja

Daga Mu'azu Hassan  @ Katsina Times

Jaridar Weekend Trust ta ranar Asabar, 25 ga Yuli, 2026, ta wallafa rahoto kan yadda 'yan bindiga ke gallaza wa al'ummomin wasu yankuna a Jihar Neja, musamman a ƙananan hukumomin Borgu, Mariga, Shiroro da sauran wurare.

A cewar rahoton, 'yan bindigar sun kakaba wa mazauna yankunan haraji na kuɗi, wanda dole ne su biya kafin a bar su su zauna lafiya tare da gudanar da ayyukan noma a garuruwansu.

Wasu daga cikin mazauna yankunan da jaridar Daily Trust ta tattauna da su sun bayyana cewa, baya ga harajin kuɗi, 'yan bindigar sun sanya wasu tsauraran sharuɗɗa. Sun ce a duk lokacin da 'yan bindigar suka ga dama, suna shiga ƙauyukan su tare da kutsa kai cikin gidajen jama'a domin yi wa mata fyade.

Mazaunan sun ƙara da cewa, a wasu lokuta ma, 'yan bindigar kan tilasta wa wasu maza su kai musu matansu zuwa cikin daji, inda ake cin zarafinsu ta hanyar fyade kafin daga bisani a mayar da su gida.

Advertisement

BSIL Security Report

Sun bayyana cewa wannan ne halin da sukke ciki a yanzu, lamarin da ya jefa al'ummomin yankunan cikin tsananin tsoro da rashin walwala.

Katsina Times 

@ www.katsinatimes.com 

Facebook page: katsina city news 

Facebook page .jaridar taskar labarai

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 5 + 3?