Ba Sani Yellow na Katsina aka kashe ba a bidiyon da ake yadawa, – Danjarida mai binciken ƙwakwaf ya fayyace gaskiya.

Katsina TimesWani danjarida mai binciken ƙwakwaf a jihar Zamfara da ke Arewacin Nijeriya, Mannir Sani Fura Girke, ya karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kashe…

Katsina City News July 15, 2026  ·  12:00 AM
| 133 Views
Ba Sani Yellow na Katsina aka kashe ba a bidiyon da ake yadawa, – Danjarida mai binciken ƙwakwaf ya fayyace gaskiya.
Ba Sani Yellow na Katsina aka kashe ba a bidiyon da ake yadawa, – Danjarida mai binciken ƙwakwaf ya fayyace gaskiya.

Katsina Times


Wani danjarida mai binciken ƙwakwaf a jihar Zamfara da ke Arewacin Nijeriya, Mannir Sani Fura Girke, ya karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kashe Sani Yellow da ya shahara a wani bidiyon sulhu da 'yanbindiga a jihar Katsina. A cewarsa, mutumin da aka kashe ba shi ne Sani Yellow na Katsina ba, illa wani daban mai laƙabin Yellow da ke aiki tare da 'yan bindiga a dajin Bagega, da ke Ƙaramar Hukumar Anka a jihar Zamfara.


Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wasu 'yanbindiga sun kai hari a yankin Dareta, da ke kan hanyar zuwa Bagega, a lokacin da ma'aikatan kamfanin MBHIS suka je yankin domin debo ƙasa da ake amfani da ita wajen aikin shimfida hanya a Ƙaramar Hukumar Anka. A yayin harin, an kashe wasu jami'an tsaro na kamfanin da aka fi sani da "yan Maiduguri", tare da wani Injiniya, yayin da direban motar ya samu raunuka sakamakon harbin bindiga. Sai dai jami'an tsaron da ke tare da ma'aikatan sun mayar da martani, inda aka yi musayar wuta mai tsanani, lamarin da ya yi sanadin kashe wasu daga cikin maharan tare da kama wani a cikinsu da ake kira Yellow.


Mannir Sani Fura Girke ya ce bayan kama shi, an kashe mutumin, sannan aka riƙa yaɗa bidiyon yadda ake jan gawarsa a bayan babur.


Ya ce kuskuren da ya jawo ruɗani shi ne yadda wasu masu amfani da kafafen sada zumunta suka ɗauki tsohon hoton Sani Yellow na Katsina, suka haɗa shi da labarin mutumin da aka kashe, ba tare da tantance gaskiyar lamarin ba.


Advertisement

BSIL Security Report

A cewarsa, hoton da aka riƙa yaɗawa na Sani Yellow na Katsina ne, wanda ya fito fili a lokacin tattaunawar sulhu tsakanin gwamnati da wasu 'yanbindiga a Ƙaramar Hukumar Dan-Musa ta jihar Katsina. Ya ce duk wanda ya kalli hoton da kyau zai lura da makirufo (mic) da ke gaban rigarsa, alamar yana cikin wata hira da kafafen yaɗa labarai a wani Sulhu.


Mannir ya jaddada cewa Sani Yellow na Katsina yana raye kuma yana cikin jihar Katsina, ba ma a Zamfara yake ba a lokacin da aka yi wannan artabu.


Ya ƙara da cewa mutumin da aka kashe matashi ne daga cikin 'yanbindigar da ke dajin Bagega, amma ba fitaccen jagora ba ne irin waɗanda aka fi sani da "Kachalla". Duk da haka, ya kasance cikin matasan 'yanbindigar da aka san suna aikata munanan hare-hare a yankin.


A ƙarshe, Mannir Sani Fura Girke ya yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta da su riƙa tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa, yana mai cewa yaɗa hotuna ko bayanan da ba su dace da ainihin lamarin ba na haddasa ruɗani, yana kuma kawo cikas ga yaƙi da yaɗa labaran ƙarya da farfaganda, har ma da yi wa harkar illa ba a farga ba.


Hoto: Hoton Sani Yellow na Katsina a yayin fira da manema labarai a wani taron Sulhu a Katsina.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 7 + 8?