RANAR MALAMAI TA DUNIYA: Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana manufar bunkasa ilimi
- Katsina City News
- 05 Oct, 2023
- 801
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Domin karrama ranar malamai ta duniya ta shekarar 2023, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ganin an farfado da harkar ilimi a jihar.
Gwamna Radda ya bayyana kudirinsa ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar, a bikin ranar malamai ta duniya ta bana, mai taken “Malaman da muke bukata domin ilimin da muke so: Ya zama wajibi a duniya don magance matsalar karancin malamai."
Ranar malamai ta duniya, wadda ake yi kowace ranar 5 ga watan Oktoba, tana girmama malamai a duk duniya, kuma ta kasance a matsayin wani lokaci don gane muhimmiyar rawar da suke takawa wajen sake fasalin ilimi.
Haka nan yana haifar da tunani game da mahimman tallafin da malamai ke buƙata don yin amfani da iya warsu da ayyukan su, da kuma tsara hanyar sa ido ga tsarin koyo da koyarwa ta Duniya
Babban abin da aka fi mayar da hankali kan ranar malamai ta duniya ta 2023 ita ce muhimmiyar bukata ta dakatar da raguwar adadin malamai da kuma shiga wani yunƙuri na duniya don ƙara darajarsu.
Gwamna Radda, ya kuma yaba wa malamai a matsayin masu fafutuka wajen tsara makomar al’umma da kasa baki daya, ya kuma yi alkawarin ba da himma ga gwamnatinsa wajen kyautata rayuwar malaman Katsina.
“A matsayi na na tsohon malamin aji, na fahimci sadaukarwa da malamai suke yi domin raya al’umma masu zuwa su zama masu koyi da juna, don haka ne gwamnatin mu za ta bayar da goyon baya ga harkar koyarwa a jihar Katsina, da zummar kawo sauyi ga tsarin ilimi na jihar mu baki daya. " Gwamna Radda ya jaddada.
Ya kuma jaddada fifikon gwamnatinsa na inganta harkar ilimi, inda ya bukaci malamai da masana ilimin jihar Katsina da kada su yi kasa a gwiwa wajen tsara makomar yara da daliban jihar.
Gwamna Radda ya bayyana jin dadinsa da irin wannan gagarumin aiki da malaman Katsina suka yi, inda ya bayyana irin gagarumin ci gaban da gwamnatinsa ta samu wajen daukaka darajar ilimi a jihar.
“Ga manyan malaman mu, ina mai tabbatar muku da cewa gwamnatin mu ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta ci gaba da bayar da horo da kuma kara karfin gwiwa, mun riga mun kaddamar da kwangilar gina wasu makarantun firamare da sakandare da dama a fadin jihar nan na miliyoyin Nairori . Samar da kayan koyo da kafa makarantun a dukkan Gundumomin Sanatan Katsina guda uku.
“Bugu da kari kuma, mun samu nasarar daukar sabbin malamai 7,000 domin karfafa ma’aikata ilimi a Katsina, haka nan kuma a shirye muke mu baiwa daliban Katsina tallafin karatu, tare da sadaukar da kai wajen inganta manyan makarantun jihar da kuma karfafa takwarorinsu na tarayya.
Gwamna Radda ya kara da cewa, “A matsayin mu na gwamnati, kudurinmu bai gushe ba a yunkurinmu na ganin mun dawo da tsarin karatun jihar Katsina kamar yadda ta kasance a nan gaba.
Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da shuni a cikin jihar da su marawa kudirin gwamnatin sa na ganin an kawo gyara a fannin ilimi na Katsina.