Maulidi: Kasuwar Cake/Filin Bugu Ta Cika Ta Batse.
- Katsina City News
- 04 Oct, 2023
- 803
Daga Mohammad A. Isah.
'Yan kasuwar dadaddiyar kasuwar nan da ke cikin Birnin Katsina da ke kan hanyar zuwa kofar Guga, Filin bugu/Cake sun shirya gagarumin Maulidin fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu(S) a ranar Larabar nan.
Kamar yadda suka saba gudanar duk shekara, a bana ma 'yan Kasuwar sun shirya gagrumin Maulidin.
Tun farko dai, dukkan masu shaguna da masu ra6awa suna kasa kaya a kan hanya a Kasuwar, sun kulle tare da nade kayansu baki daya tun daga Miasalin karfe 2:00 na rana, inda daga nan kuma kowa ya soma kawata matsugunninsa ko shagonsa aka fara tudadowa aiwatar da taron Maulidin.
Dafifin mutane da suka rika tururuwa zuwa taron a Kasuwar ya zarce tururuwar da munane ke yi zuwa cin kasuwar a ranakun da take babban ci wato ranakun Talata da Juma'a.
Duk inda ka gitta jama'a ne kashi-kashi; wasu na zikirori, wasu na yin karatun Ishiriniya, wasu na Wakokin yabo ga Manzon Allah(S), wasu kuma na zuwa da komowa daga farkon kasuwar zuwa karshenta suna karatuttuka, zikirori da kuma wakokin yabo ga Annabi Muhammad(S)
A lokacin da na zagaya kasuwar, na ga wasu rukunin al'umma sun kawata Majalisinsu; wasu sun saka tsadaddin kaya da manya-manyan Shaddodi wadanda aka kashewa manyan kudafe, wasu kuma sanye da wasu nau'ikan kaya .
Masu aiwatar da da taron Maulidin, wasunsu suna tafiya suna fesa turaruka ga 'yan kallo da wadanda suka gayyato, wasu suna kunna tsintsiyar kamshi, wasu suna raba abinci, wasu na raba kullikan kayan tande-da-makulashe, akwai ma masu raba shayi kofi-kofi.
'Yan kallo kuwa duk sun fito a kan hanya suna kallo; wasu a kan benayen danke layin Kasuwar, wasu kuma na lekowa daga zaurukan gidajensu.
A zantawar da muka yi da wasu daga cikin masu Maulidin sun nuna jin dadinsu bisa ga yadda Allah ya kara nuna masu wannan rana da suka zuba dukiyarsu wadda ba a bakin komai bace tun da a kan hidima ga Manzon Allah(S) aka zuba ta.
'Yan kallon ma sun bayyana mana irin farin cikinsu bisa ga yadda suka zo suka halarci wannan taro na Maulidi da 'yan Kasuwar suka shirya sakoba Annabi(S).