An yi Bikin Yaye Daliban Madarisatul Hizburraheem Funtua A Karo na 23.

top-news

Muhammad Ali Hafiziy, Katsina Times 

A ranar Lahadi, 26 ga watan Janairu, 2025, aka gudanar da bikin yaye daliban Madarasatul Hizburraheem da ke karkashin jagorancin Khalifa Sheikh Aliyu Sa’idu Abubakar Alti Funtua. Taron ya gudana a filin Aya, cikin garin Funtua a jihar Katsina, inda ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen jihar Katsina.

Bikin ya samu halartar fitattun mutane, ciki har da wakilin Gwamnan jihar Katsina, Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abdullahi Garba Faskari; Mai Alfarma Sarkin Musulmi, (Dr.) Sa’ad Abubakar; tsaffin dalibai, ’yan siyasa, ’yan kasuwa, da sauran al’umma. Wannan ne karo na 23 da makarantar ke gudanar da irin wannan bikin tun lokacin kafuwarta.

A wannan shekarar, makarantar ta yaye dalibai guda 32 da suka haddace Al-Qur’ani mai girma, yayin da dalibai 582 suka kammala sabkar Al-Qur’ani. Haka kuma, matan aure guda 30 sun halarci taron domin nuna bajintar su wajen haddar Al-Qur’ani mai girma.

A jawabin da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, (Dr.) Sa’ad Abubakar, ya gabatar, ya yabawa kokarin malamai da daliban makarantar kan jajircewarsu da sadaukarwarsu har suka kai ga samun wannan nasara. Ya bayyana cewa, “Na ji dadi sosai da na halarci wannan taro mai albarka, domin kuwa na ga dalibai masu yawa wadanda suka Haddace Al-Qur’ani mai girma. Wannan babban ci gaba ne ga al’umma.”

Sarkin Musulmi ya kuma kara jaddada muhimmancin karatun Al-Qur’ani da haddarsa a tsakanin matasa, yana mai cewa wannan shi ne tushen ci gaban al’umma, da hanyar samun jagoranci mai tsafta da amana.

Shi ma, a nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, da ya wakilci Gwamnan jihar Katsina a wajen bikin, ya bayyana jin dadin sa kan yadda harkar ilimin addini ke samun cigaba a jihar. Ya ce, “Gwamnatin Jihar Katsina tana kara bai wa harkar ilimin addini muhimmanci, ta hanyar tallafa wa irin wadannan makarantun muhimmanci, don ci gaban ilimi a jihar.” 

Ya kuma bayyana farin cikinsa da halartar wannan taro, yana mai cewa abubuwan da ya shaida sun kara masa kwarin gwiwa kan jajircewar al’umma wajen ci gaban addini da ilimi.

Bikin yaye daliban Madarasatul Hizburraheem ya zama wani gagarumin abu a cikin al’ummar Funtua, inda ake amfani da irin wannan dama don karfafa gwiwar iyaye da matasa kan muhimmancin karatun Al-Qur’ani. Malaman makarantar sun bayyana cewa ci gaban da suka samu ba zai yiwu ba tare da goyon bayan iyaye da sauran al’umma ba.

A karshen taron, an yi addu’o’i na musamman domin fatan samun ci gaba da kuma samun alheri ga dukkan daliban da suka halarci wannan makaranta. Wannan biki na yaye dalibai ya tabbatar da cewa makarantar ta zama madubin koyarwa da koyi a yankin, musamman a fannin haddar Al-Qur’ani mai girma.