NA GA TSOHUWAR DAULAR ISIS.

top-news

@ katsina times 
@jaridar taskar labarai 

A kasar Iraq nayi tafiya cikin tsohon yankin da ISIS suka tafa kafawa wadda suna gab da kwace kasar Iraqi,Al ummar kasar suka tashi tsaye suka kwaci kansu.

Na ratsa garuruwan Falluja,Mosul,Tikrit  har zuwa Sammara.
Naga yadda yan ISIS suka rugurguza kauyuka da birane.
Darasin Iraqi yana da kwatankwaci da halin da kasar mu take ciki na rashin tsaro har da jahar katsina.
Mutanen Iraqi basu kwaci kansu daga ISIS ba. Sai da kowa ya zama soja.suka kafa wata runduna mai suna rundunar al umma.
Daga wuraren da ISIS suka kwata har da wani bangare na birnin Baghdad.  Misali unguwar khazimiyya dake gefen Baghdad. 

Naje Hubbare Imam musa Al kazim( as) daya daga cikin jikokin Manzon Allah ( saw) naga hotunan yadda ISIS sukayi raga da raga da wurin kafin a fara  gyaran shi.

A Sammara naje hubbare  Imam Musa Al askari( as) daya daga cikin jikokin Manzon Allah(saw) shima naga hotunan yadda aka ragargaza shi kafin a fara gyara.

A Iraq na kara samun gamsuwar matsalar tsaro sai al umma  sun dau mataki akan kan su da sa idon gwamnati  da jami an tsaro,Kafin ayi nasara.sai da kowa ya zama soja iraqawa suka kwaci kansu daga ISIS. Wane darasi zamu dauka daga halin da muke ciki na kauraye da Bandits?
Www.katsinatimes.com 
Www.jaridartaskarlabarai.com