"NA ZIYARCI BANGON KISRA DA KABARIN SALMAN FARISI".
- Katsina City News
- 22 Sep, 2023
- 1111
@ Katsina Times
Jaridar Taskar Labarai
Yazo a Tarihin Musulunci Ranar da aka Haifi Manzon Allah (s.a.w) Abubuwan Al ajabi sun faru a Duniya, wanda ya nuna Isharar cewa an Haifi Mai Daraja.
Daga ciki Abubuwan Isharar da suka faru, akwai Tsagewar Bangon Kisra.
Wannan Tsagaggen Bango, Allah ya tsare wannan bangare har yanzu yana nan gefen Birnin Baghdad.
Gwamnatin kasar Iraqi da hadin gwaiwar Jami' ar Pennsylvania dake kasar Amurka sun killace shi suna kula dashi, domin Maziyarta daga ko'ina a Duniya.
Na ziyarci wannan Bango, Bangon yana a bayan Hubbaren Sahabin Manzon Allah (s.a.w) Salmanul Farisi da wasu sahabai guda uku.
Na ziyarci Kaburburan wadannan Sahabbai na kuma ziyarci Bangon Kisra.
@ www.katsinatimes.com
@ www.jaridartaskarlabarai
All in All SOCIAL media platforms.
07043777779 08057777762