PDP A Katsina Ta Yi Taron Bayyana Matsayarta Game Da Jita-jihar Hadewarta Da Sabuwar Jam'iyyar Hadaka.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13072025_154745_FB_IMG_1752421602753.jpg


Jam'iyyar PDP ta jihar Katisna a ranar Lahadin nan 13 ga Yulin 2025, a wani taro da ta kira na masu ruwa da tsaki a jam'iyyar daga daukacin kananan hukumomin jihar 34 a Hedikwatarta na jiha, ta bayyana matsayarta game da rade-radin da ta ce an fara yadawa kan cewar jiga-jiganta suna shirin komawa sabuwar jam'iyyar hadaka ta ADC.

A yayin da yake gabatar da makasudin taron, Sakataren gudanar da shirye-shiryen jam'iyyar na Jiha, Honorabul Ali Haro ya tabbatarwa mahalarta taron cewar, bayan tarukan tattauna da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a cikin gida da waje a matakan, Mazabu, kananan hukumomi da jiha baki daya, duk sun samu matsayar a kan tabbatuwarsu a kan jam'iyyarsu ta PDP babu gudu ba ja da baya.

Makasudin wannan taro shi ne don mu tabbatar maku cewar 'yan kwamitin zartaswa, 'yan kwamitin kanan hukumomi, da na 'Wards' da sauran eldojinmu muna bayyana wa duniya mun ittifaki babu abin da muke yi sai jam'iyyar PDP!" Ya tabbatar

Ya ce, tara al'ummar jam'iyyar ta PDP a kan wannan matsayar tasu ya zama dole don kauda rudani da jita-jitar cewar wani bangare nasu na kokarin barin jam'iyyar don tafiya jam'iyyar hadaka, inda ya sake bayyana hakan a matsayin labarin kanzon kurege.

Shi ma nashi jawabin tabbatuwar tasu a jam'iyyar ta PDP, shugaban jam'iyyar PDP ta jiha, Honorabul Nuraddeen Amadi Kurfi ya ba wa al'ummar da suka taru cewar tun daga matakin kasa, jihohi da kanan hukumomin jihar, jam'iyyar ta PDP da jiga-jiganta na nan daram a cikinta, yana mai bayyana jam'iyyar da cewar ita kadai ce ta al'umma ba kawai a fadin jihar Katsina ba, har ma da kasa baki daya don haka, "jam'iyyar PDP ba za ta mutu ba a Nijeriya."

Horobaul Kurfi, ya ce duk da halin da jam'iyyar ta PDP ta shiga tsawon shekaru 10 da suka gabata, amma ko a zabukan shekarar 2023 jam'iyyar ta ci wasu zabuka a matakan kananan hukumomi, Majalissun jiha da Majalissun kasa, yana mai cewar ko a nan "Jam'iyyar PDP ta fi karfin ta narke a cikin wata jam'iyya.

"Muna ba ku tabbacin cewar jam'iyyar PDP ashekarar 2027 za ta shiga zabe a dukkan mazabu." Ya jadda.

Jigo a jam'iyyar a jihar, a yayin jawabinsa na babban bako a taron, Sanata Yakubu Lado Danmarke, ya bukaci al'ummar da suka taru a wajen, da su je su bayyana wa sauran magoya baya waadanda ba su samu halarta taron ba wannan matsayar tasu wadda suka kira taro don bayyana ta, inda ya bayyana masu yada cewar su 'yan PDP din ne amma suka tafi zuwa jam'iyyar hadaka a matsayin 'ya'yan wake mai yado babu 'ya'ya, yana mai zarginsu da wadanda suka sha kaye a rumfunansu ashrkarar 2023.

Taron bayyana matsayar na PDP dai, ya samu halartar masu ruwa da tsaki na jam'iyyar, Magoya baya daga daukacin kananan hukumomin jihar, da wasu rukunin mata da suka canja sheka daga APC zuwa PDP wadanda jigo na matan jam'iyyar, Shamsiyya Mustapha (Shama Kamshi) ta kawo wa jam'iyyar.

Follow Us