"Duk Wanda Yace Jam'iyyar PDP Ta Mutu A Jihar Katsina Karya Yake! Sai Dai Idan Shi Ne Ya Mutu" -Hon Aminu Chindo.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12072025_204627_FB_IMG_1752353098546.jpg


‎Daga: Muhammad Ali Hafizy |Katsina Times.
‎A wani taron kara jaddada goyon baya ga jami'yar PDP wanda kungiyar "PDP Restoration Project Katsina State " ta shirya, karkashin jagorancin Hon. Aminu Ahmad Chindo (Sadaukin Katsina) a ranar Asabar 12 ga watan Yuli 2025, an kara jaddada goyon baya dari bisa dari ga jam'iyyar.
‎Taron wanda ya samu halartar manyan yan siyasar jam'iyar, wadanda suka haɗa da, shugaban jam'iyar na jihar Katsina Hon. Nura Amadi Kurfi, shugaban jam'iyar na shiyar Katsina, Hon. Sanusi Abdullahi Fari, shugaban matasa na jam'iyar Hon. Nura VC Dutsinma, Alhaji Shehu Muhammad, Hon. Ibrahim Galadima, Alhaji Hassan Maiwake da sauransu.
‎A cikin jawabin da Chindo ya gabatar a wajen taron, ya jaddada aniyarshi ta cigaba da zama a jam'iyar PDP daram, ba tare da canza sheka ba, ya kuma yi watsi da duk wata tafiya da ake kokarin yi a jihar tare da tabbatar da nasarar jam'iyar PDP a zabe mai zuwa.
‎"A zaben 2023 kuri'ar Katsina itace ta sanya jam'iyar PDP tayi rinjaye aka samu dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya ci Katsina, duk wanda yace PDP ta mutu sai dai idan shine ya mutu, har yanzu PDP na nan da ranta, kuma duk wanda yace wani ya mutu to shine ya mutu ba wancan din ba" inji shi.
‎Ya kara jaddada aniyar shi ta sake tsayawa takara a zabe mai zuwa sannan yayi ikirarin cewa  kujerar dan majalissar tarayya mai wakiltar Katsina kujerar shi ce kuma zai tabbatar da hakan a zabe mai zuwa, ya kuma kara a cewa kwace mashi ida da akayi ba baya, anyi kuskuren da ba za'a sake maimaita mashi shi ba.
‎Shugaban jam'iyar PDP a jihar Hon. Nura Amadi Kurfi ya mika jinjina da godiya ga Chindo a bisa irin abubuwan alkairin da yaka gudanarwar a fadin jihar Katsina baki daya, sannan ya jinjina mashi wajen kokarin da yake yi na kara cigabantar da jami'yar da kuma tabbatar mata da nasara a zabe mai zuwa.
‎Bugu da kari a yayin gudanar da taron, wasu gungun matasa wadanda Chindo ya samar ma aiki a ma'aikatu Road Safety, Fire Service, Civil Defence, Immigration, sun karramashi da lambar girmamawa, tare da jinjina da kuma yabo gareshi na irin rawar da ya taka har suka samu aikin.

Follow Us