Gwamna Radda Ya Dakatar da Ma’aikatan Gandun Daji Bisa Zargin Mamaye Daji a Ingawa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12072025_232032_FB_IMG_1752362339524.jpg

Daga Wakilinmu na Katsina Times
12 ga Yuli, 2025

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayar da umarnin dakatar da wasu manyan jami’an kula da gandun daji tare da kaddamar da bincike mai zurfi kan zargin mamaye da killace dajin da ke kauyen Manomawa, a ƙaramar hukumar Ingawa.

Wannan matakin ya biyo bayan korafi daga ƙungiyar al’adu da walwalar Fulani ta Kautal Hore (Kautal Ja’onde Jam) reshen Jihar Katsina, wadda ta zargi wasu da mamaye filayen kiwo da hanyoyin shanu da kuma dajin da aka tanada na musamman a yankin.

A Matsayin tabbatar wa, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, ya jagoranci wata tawaga zuwa wurin domin duba lamarin. Tawagar ta haɗa da Shugaban Karamar Hukumar Ingawa, jami’an ‘yan sanda, jami’an DSS da wakilan masu ƙorafin.

Binciken da suka gudanar ya tabbatar da cewa an share filin dajin domin fara noman bana, tare da gano wasu abubuwan da suka nuna cewa an yi rabon filayen ba bisa ka’ida ba. Jami’an da binciken ya shafa sun haɗa da Mai garin Manomawa, Jami’in Gandun Daji na Kankiya, Shuaibu Gambo, da Shugaban Sashen Gandun Daji na Ingawa, Saidu Danjuma.

Sakamakon haka, Gwamna Radda ya bayar da umarnin dakatar da Shuaibu Gambo da Saidu Danjuma nan take, domin bai wa bincike damar tafiya ba tare da katsalandan ba.

Haka zalika, ya umarci Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Katsina da ta gudanar da cikakken bincike kan ayyukan Jami’in Gandun Daji na Kankiya, tare da ɗaukar matakin ladabtarwa idan an samu laifi. Har ila yau, Hukumar Kula da Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Jihar Katsina ta samu umarnin binciken shugaban sashen gandun dajin Ingawa domin ɗaukar mataki idan ya dace.

Gwamnatin ta kuma buƙaci Majalisar Masarautar Katsina da ta gudanar da bincike kan rawar da mai garin Manomawa ya taka a lamarin, tare da ɗaukar matakin da ya dace.

Gwamnatin Jihar Katsina ta jaddada kudurinta na kare albarkatun jama’a da na ƙasa, da tabbatar da gaskiya da gaskiya a dukkan matakan mulki, da kuma ɗaukar matakin da ya kamata kan duk wani abu da zai haifar da rikici tsakanin manoma da makiyaya, domin ci gaba da samar da zaman lafiya da ɗorewar muhalli.

Follow Us