Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | KatsinaTimes
Hukumar Ilmin Firamare ta Jihar Katsina (SUBEB), tare da hadin gwiwar Hukumar Ilmin Firamare ta Kasa (UBEC), sun fara wani gagarumin shirin horas da ma’aikatan ilimi kan amfani da na'urar zamani (tablets) a matsayin wani bangare na shirin Transforming Education Systems at the State Level (TESS). An fara horaswar ce a ranar Litinin, 23 ga Yuni, 2025, a dakin taro na Katsina Guest Inn.
Wannan shirin na kwanaki shida na karkashin shirin Better Education Service Delivery for All Additional Financing (BESDA-AF) wanda Bankin Duniya ke daukar nauyinsa, kuma an tsara shi ne domin inganta fahimtar karatu da rubutu a makarantun firamare ta hanyar amfani da fasaha da horar da malamai.
An zabi kwararrun masu horaswa guda 85 domin koyar da sauran Ma’aikatan Tallafin Makarantu (SSOs) da malamai a fadin kananan hukumomi 34 na jihar.
Da take jawabi wajen bude taron, Uwargida Ummulkhairi Ahamed Bawa, Sakatariyar Dindindin a Ma’aikatar Ilimi ta Firamare da Sakandare, wadda ta wakilci Kwamishinar Ilimi, Hajiya Zainab Musa Musawa, ta bayyana cewa:
"Wannan horaswa ba wai taro bane na yau da kullum. Mataki ne na dabarar sauya fasalin ilimi a jihar mu."
Ta ce karatu da fahimta sune ginshikan kowane fanni na ilimi, kuma ta bukaci mahalarta da su dauki horaswar da muhimmanci sosai.
Ta jinjinawa UBEC da tawagar kasa da kasa karkashin jagorancin Dr. Alishin, tare da tabbatar da cewa gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umar Radda na jajircewa wajen sauya tsarin ilimi.
A nasa bangaren, Rabiu Idris, mamba a hukumar SUBEB da ya wakilci Shugaban hukumar, ya bayyana cewa yanzu ana amfani da fasahar zamani wajen bibiyar ci gaban makarantu, wanda ya hada da amfani da dashboard, checklist da application na wayar hannu.
"Ba wai kawai gyara tsarin koyarwa muke yi ba, har da tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkar ilimi," inji shi.
Ya ce gwamnatin jihar ta gina da gyara dakunan karatu sama da 1,000 tare da daukar malamai fiye da 7,000 da aka tura yankunan karkara. Har ila yau, an fitar da kudaden tallafin inganta makarantu (School Improvement Grant) da suka taimaka wajen samar da kayan koyo da gyaran kayayyakin makarantu.
Shugaban shirin BESDA-AF na kasa, Alessi Olumayowa, ya bayyana cewa wannan shiri mai dauke da dala miliyan $123.8 yana mayar da hankali kan jihohin Oyo, Adamawa da Katsina da ake kira jihohin OAK.
"Katsina ce ta fara aiwatar da wannan horaswa daga cikin jihohin OAK. Muna sa ran ganin tasirin aikin malamai da aka horar bayan wannan lokaci," inji Olumayowa.
Shirin na BESDA-AF yana bai wa jihohi tallafi ne bayan sun cika wasu sharudda na aiki da ake kira Disbursement-Linked Indicators (DLIs).
Ko’odinetan TESS a Katsina, Binta Abdulmumini Ahamed, ta bayyana cewa an raba shirin horaswar zuwa matakai biyu:
Kwanaki 1 zuwa 3: Za a mayar da hankali ne kan koya wa mahalarta yadda ake amfani da na'urar zamani da sauran manhajojin dijital.
Kwanaki 4 zuwa 6: Za a ci gaba da horas da SSOs tare da masu ruwa da tsaki daga kasashen waje kamar Kanada da Amurka.
Manufar shirin ita ce koya wa jami’an ilimi dabarun amfani da fasahar zamani, gano bukatun malamai, da amfani da tsarin nazarin aiki domin tabbatar da ingantacciyar koyarwa a makarantu.
Dukkan masu ruwa da tsaki sun bukaci mahalarta da su dauki shirin da mahimmanci tare da yada ilimin da suka samu zuwa cikin kowane aji, makarantun firamare da kuma cikin al’umma baki daya.
Haka kuma, an bayyana godiya ga dukkan masu halarta ciki har da jami’an gwamnati, malamai, malaman addini da kungiyoyi masu ruwa da tsaki.