
Honorable Aminu Bale Dan Arewa
Daga Wakilin mu
A ranar Asabar, 24 ga Mayu, 2025, wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar APC a kananan hukumomin Kurfi da Dutsinma sun halarci taron da aka gudanar a cibiyar hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomi ta jihar Katsina, inda suka tattauna kan matsayin jam’iyyar da kuma goyon bayan gwamna Dikko Umaru Radda.
Taron wanda ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Hon. Aminu Balele Dan Arewa, ya jagoranta, ya samu halartar shugabanni daga matakin mazabu har zuwa na ƙaramar hukuma. A jawabinsa, Dan Arewa ya bayyana cewa wakilan majalisar tarayya su 18 na jam’iyyar APC sun yi taro a Abuja, inda suka nuna goyon bayansu ga Gwamna Radda da ya sake tsayawa takara a 2027.
Ya bayyana ayyukan ci gaba da gwamnan ke aiwatarwa a matsayin dalilin wannan matsaya, yana mai cewa al’ummar yankin Kurfi da Dutsinma sun gamsu da irin jagorancin da Gwamna Radda ke bayarwa.
A cikin wannan taro ne kuma Hon. Dan Arewa ya raba tallafin kuɗi kimanin naira miliyan 15 da dubu 980 ga shugabannin jam’iyyar domin saukaka musu bukukuwan Sallah da ke tafe.