Ministan Gidaje Ya Yaba Wa EFCC Kan Wani Katafaren Gini Da Ta Kwace a Abuja

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes21052025_170501_FB_IMG_1747847043963.jpg

Katsina Times 

Ministan Gidaje da Raya Birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ya jinjina wa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) bisa kwazonta na karbo kadarori da aka wawure a sassa daban-daban na kasar nan, musamman wasu katafaren gine-gine guda 753 da ke unguwar Lokogoma a Abuja da aka mika wa gwamnati.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 21 ga Mayu, 2025, yayin da ya jagoranci duba wannan kadarar da ke filin lamba 109, Cadastral Zone C09, Lokogoma District, mai fadin murabba’in mita 150,500, wadda ta kunshi gidaje 753 ciki har da duplex da sauran nau’ikan gidaje. An karbo kadarar ne bisa umarnin karshe na kotun Babbar Kotun Birnin Tarayya da mai shari’a Jude Onwuegbuzie ya bayar a ranar 2 ga Disamba, 2024.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Minista Dangiwa ya bayyana wannan karbo kadarar a matsayin abin tarihi. Ya ce: “Ina matukar yabawa da jajircewar shugaban EFCC, Mista Ola Olukoyede, bisa wannan bajintar. Wannan shi ne mafi girma daga cikin kadarorin da aka taba karbo wa gwamnati a tarihin kasar nan. Gidaje 753 aka samu a cikin shekara daya da nada shugaban EFCC. Akwai karin kadarorin da ake ci gaba da karbo wa, kuma muna tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za su ci gajiyar wannan namijin kokari.”

Ya kuma bukaci ‘yan kasa da su ci gaba da marawa EFCC baya wajen yaki da cin hanci da rashawa. “Ina kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yarda da kokarin shugaban EFCC. Na tabbata yana samun kwarin guiwa daga shugaba kasa, wanda ya ba shi cikakken damar gudanar da aikinsa, kuma yana amfana da wannan dama sosai,” in ji shi.

A nasa bangaren, shugaban EFCC, Mista Olukoyede, ya jaddada kudirin hukumar na ci gaba da yin aiki da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da kadarorin da aka karbo. Ya bayyana cewa wannan ziyara na da nasaba da mika kadarar ga Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane.

“A jiya muka gana da mai girma Minista kan mika wannan kadarar, kuma mun yanke shawarar zuwan nan domin ‘yan Najeriya su gani da idanunsu. Mun shafe fiye da awa daya muna zagaye, amma har yanzu ba mu gama ziyartar dukkanin wuraren ba. Wannan ya nuna girman kadarar da muka karbo,” in ji shi.

Shugaban EFCC ya bayyana cewa kodayake an bayyana adadin gidaje 753 ne, adadin zai iya karuwa bayan sake fasalin gine-ginen. “Adadin da muka bayar na farko ya dogara da zane da bincike na farko. Bayan sake fasalin, akwai yiwuwar samun karin gidaje. Amma abin da yafi muhimmanci shi ne, yanzu kadarar ta dawo hannun gwamnatin tarayya ne, kuma za a yi amfani da ita yadda ya dace,” in ji Olukoyede.

Ya ce wannan nasara wata hujja ce ta aiwatar da tsarin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ke amfani da yaki da cin hanci a matsayin hanyar habaka tattalin arziki.

“Wannan na daga cikin shaidu na hangen nesa na Shugaban kasa, wanda ke amfani da yaki da rashawa domin karfafa tattalin arzikin kasa. Bayan sake fasalin, gwamnati za ta zartar da yadda za a yi amfani da su, ko da zai kai ga bai wa ‘yan Najeriya masu kishin kasa damar mallakar gidaje cikin gaskiya da adalci,” in ji shi.

Daga karshe, shugaban EFCC ya tabbatar da kudirin hukumar na ci gaba da yaki da laifukan tattalin arziki da kudi ba tare da nuna bangaranci ba.

Follow Us