AL'UMMAR MAZABAR DAN'ALHAJI/YANGAYYA, A BATSARI SUN KOKA KAN YUNKURIN DAKATAR DA YAYANSU CIGABA DA RUBUTA JARABAWAR WAEC A MAKARANTAR GSSS YANDAKA RUMA.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes19052025_145907_IMG-20250519-WA0063.jpg

AL'UMMAR MAZABAR DAN'ALHAJI/YANGAYYA, A BATSARI SUN KOKA KAN YUNKURIN DAKATAR DA YAYANSU CIGABA DA RUBUTA JARABAWAR WAEC A MAKARANTAR GSSS YANDAKA RUMA.    

Abdullahi isah @ Katsina times 

Al'ummar mazabar Danalhaji/Yangayya dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina, sun koka kan zargin dakatar da yayansu cigaba da rubuta jarabawar kammala makarantar sakandire, WAEC, 2025, a makarantar Government Senior Secondary School Yandaka Ruma, saboda kasa biyan kudin tara da ake bin makarantar.

A kwanukan baya, hukumar jarabawar WAEC ta ba makarantar takardar tara ta naira dubu dari biyar, N500,000.00 saboda zargin wasu kurakuran jarabawa, a shekarar, 2022.

Dalili kenan da yasa kungiyar iyayen yara da tsofaffin daliban makarantar suka mike tukuru domin lalubo bakin zaren.

Sun kara da cewa tun daga lokacin da aka ba makarantar takardar tarar, hukumar makarantar ke ta kokarin lalubo hanyar samun kudin, amma haka bata cimma ruwa ba.

Sun bayyana cewa yanzu haka hukumar ta aika ma makarantar takardar dakatar da rubuta jarabawa ta wannan shekarar, 2025, daga ranar 19-05-2025, sai sun biya kudin.

Don haka suke rokon al'umomin karamar hukumar Batsari da ma kasa baki daya da su kawo masu daukin gaugawa domin ba yaransu damar cigaba da rubuta jarabawarsu.

Dama hukumomin jarabawa kan aika da takardar gargadi ko tara ga makarantun da suke zargi da aikata kurakuran jarabawa.

Follow Us