Bayan da wani matashi dan shekara 33 dan Kasar Japan mai suna Honkon ya yi tarin kudi na tsawon shekaru 10 don siyan motar da yake mafarkin siya, na wata sabuwar mota Kirar Ferrari 458 Spider, sai ya zauna yana kallon yadda motar take Konewa cikin sa'a daya da tuka ta a karon farko.
Kafofin sada zumunta na Kasar Japan sun yi sharhi game da rahoton bakin ciki na Honkon, matashin da ya kasance mai shirya wakoki, wanda ya kashe makudan kudi game da mafarkin sayan motarsa ta Ferrari, sai dai ya kalle ta tana ci da wuta a ranar da ya tuka ta a karon farko.
Dan shekara 33 kwanan nan ya dauki hankalin mabiya manhajar ‘D (Twitter) don yada labarin kan yadda zai ji dadin gaskata mafarkin mallakar Ferrari a ‘yan mintuna Kadan kawai ta kama da wuta yayin da yake tuki a kan babbar titin Shuto a Tokyo, Laraba, 16 ga Afrilu.
A bayyane yake, an kawo masa zabinsa Spider 458 ne kawai, kuma yana cikin motar kan gwajin tare da shi lokacin da ya lura da fitar wani farin hayaki. Da farko ya dauka hayakin daga motar da ke kusa da tasa motar yake fita, amma yayin da mota ta yi gaba, sai ga shi hayakin yana fitowa daga cikin motar Ferrari. Don haka sai kawai Honkon ya janye, ya fita daga cikin motar, ya kira hukumar kashe gobara. Ya kwashe mintuna 20 yana kallon burinsa ta kone kusan gaba daya.
“Ina tsammanin Ni kadai ne mutum a Japan da ya taba fuskantar irin wannan matsala,’ Honkon ya rubuta a shafin ‘D, tare da taken hoton motar da ke Konewa.
“Na kashe Yen miliyan 43 kwatankwacin (Naira miliyan dari 4 da miliyan 92 dubu dari 283 da 620), kuma abin da na samu shi ne wannan hoton."
Rundunar ’yansandan birnin Tokyo ta sanar da cewa, babu alamun karo a jikin motar Honkon ta Ferrari, amma ana ci gaba da gudanar da bincike. An yi imanin cewa gobarar ta tashi ne a cikin injin motar, amma har yanzu ba a san dalilin ba.
Yayin da a fili yake matashin ya yi bakin cikin rashin motarsa, Honkon ya shaida wa mabiyansa cewa ya yi farin ciki da ya rayu, domin yana tsoron cewa motar za ta iya fashewa yana ciki.
-Mun ciro daga jaridar Aminiya, bugun Juma'a 16 ga Mayu, 2025