SHUGANNIN MA'AIKATA NA NIJERIYA NA GUDANAR DA TARON NAZARI DA TATTAUNA DABARUN AIKI A KATSINA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13052025_175456_FB_IMG_1747158806089.jpg

Shugaban Ma'aikata na Jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale ya jagoranci sauran Shgabannin Ma'aikata na jihohi daban- daban zuwa yawon bude ido a shahararriyar Hasumiyar Gobarau mai tsawon kafa 50, wacce aka gina tun 1348 a cikin birnin Katsina.

A cikin wadanda suka zagaya da bakin akwai Kwamishinan Yada Labarai da Al'adu Dr. Bala Salisu Zango wanda mamba ne a Babban Kwamitin shirya taron kuma Shugaban karamin Kwamitin yada labarai. Har wa yau akwai Babban Sakataren bangaren harkokin mulki, Alhaji Lawal Suleiman Riko.

Bakin, sun zo Katsina ne domin halartar Taron Yini - Daya na yin Nazari da Tattauna Dabarun Aiki (Retreat) na Shugaban Ma'aikata na Tarayya tare da na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Za a gudanar da taron ne a ranar Talatar nan 13/5/2025 a dakin taro na Otel din Hill Side dake Katsina a karkashin jagorancin shugabar Ma'aikata ta Tarayya, Mrs. Didi Esther Walson - Jack.

Ana sa ran Gwamnan Jihar, Malam Dikko Umaru Radda zai kasance Babban Bako na Musamman da zai kaddamar da taron.

Abdullahi Aliyu Yar'adua 
Director Press, 
 SGS Office

Follow Us