Tabbas an kawo takardar neman karin Masarautu a Majalissar dokokin jihar Katsina, -Mai magana da yawun Kakakin Majalissar Dokokin Jihar.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13052025_150251_FB_IMG_1747148540899.jpg


Daga Auwal Isah Musa.

Ofishin mai magana da yawun shugaban majalissar dokokin jihar Katsina, ya tabbatar da an kawo Takardar neman karin Masarautu a Masarautar jihar Katsina, kodayake jami'in ofishin ya ce bai gan ta ba da idonsa ba tukunna.

Da yake zantawa da Katsina Times a ranar Talatar nan, mai magana da yawun shugaban majalissar Dokokin ta jihar Katsina, ya ce firar da ya yi da DCL Hausa a ranar Litinin inda ya ce ba a kawo ta ba, a lokacin ya tashi daga ofishi ne bai san an kawo ba.

Ya kara da cewar, wannan batu ba wani abu ba ne; in wasu Mutane, kungiyoyi ko ma daidaikun al'umma suna da kudiri ko koke ko neman wani abu suna iya gabatarwa Majalissar domin a duba shi, alabasshi sai majalissa ta duba ta yanke hukunci, inda ya ce hatta irin wannan kudiri.

Duk a kan batun, har wayau, wasu majiyoyi daga Majalissar Dokokin sun kara tabbatarwa Katsina Times cewar lallai Takardar ta je, kuma an karbe ta har ma kuma an mika ta a gaban teburin ofishin shugaban Majalissar.

In dai kuna bibiyarmu, Katsina Times ta wallafa maku labarin wata takardar neman bukatar karin wasu masarautu a masarautar Katsina wadda wasu mutane suka rubuta, inda a ranar Litinin din nan muka sakar maku takardar dauke da hatimin Majalissar Dokokin wanda hakan ke tabbatar da cewar takardar ta isa Majalissar kuma an karbe ta.

Mun halarci zaman majalissar na yau Talata don jin ko za a gabatar da takardar, amma har aka kammala babu alamun hakan tukunna, watakila sai wani lokaci.

Follow Us