Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Katsina, Kwamanda Maxwell Kaltungo Lede, ya bayyana aniyarsa ta sauya fasalin gudanar da tsaro a titunan jihar domin rage yawan hadurra da asarar rayuka.
A wata tattaunawa da Katsina Times ranar Litinin 12 ga watan Mayu 2025, Kwamanda Lede, wanda ya fito daga jihar Gombe, ya bayyana cewa ya iso Katsina ne kimanin kwanaki biyar da suka gabata, bayan da aka tura shi a matsayin sabon kwamandan hukumar a jihar. Ya ce duk da cewa ba shi da masaniya kai tsaye kan jihar kafin zuwansa, ya samu kyakkyawar tarba da kwanciyar hankali.
"Katsina jiha ce mai karamci da zaman lafiya, ba kamar yadda ake yadawa a kafafen sada zumunta ba. Na samu kwanciyar hankali kuma na yaba da irin cigaban da gwamnatin jiha ke samu, musamman a bangaren gine-ginen hanyoyi," in ji Kwamanda Lede.
Ya kara da cewa, gwamnatin jihar Katsina na da cikakken kishin lafiyar al'umma, musamman ta hanyar inganta ababen more rayuwa da tabbatar da tsaron rayuka a tituna.
Dangane da shirin da ya ke dashi a matsayin sabon kwamanda, Kwamanda Lede ya ce zai kara karfafa wayar da kan al'umma dangane da amfani da tituna cikin kwarewa da kiyaye dokokin hanya. Ya ce za su kai wannan sakon zuwa kasuwanni, wuraren ibada da cibiyoyin taro, tare da hadin gwiwar kafafen yada labarai.
Bugu da kari, Kwamanda Lede ya bayyana cewa yana shirin gudanar da bincike na musamman a fadin kananan hukumomin 34 da ke jihar domin gano wuraren da ake yawan samun hadurra (black spots), domin mika rahoton ga gwamnatin jihar don daukar mataki.
A cewarsa, "a halin yanzu, FRSC na da ofisoshi guda biyar kacal a fadin jihar, wanda bai wadatar ba idan aka kwatanta da yawan al'umma da girman jihar. Don haka muna bukatar karin ofisoshi da wuraren aiki domin samun saurin kai dauki lokacin da hadurra suka faru."
Kwamanda Lede ya kuma jaddada bukatar hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa tsaron hanyoyi ya zama aikin kowa. Ya ce zai tuntubi sauran hukumomin gwamnati da na tsaro domin yin kawancen aiki, tare da kokarin hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Katsina.
Dangane da kulawar da gwamnati ke bai wa wadanda suka ji rauni a hadurra, Kwamanda Lede ya ce akwai wani shiri da gwamnatin tarayya ta kafa wanda ake kira NEMSAS, wanda ke bayar da kulawar lafiya kyauta ga wadanda suka ji rauni a hadurra cikin sa’o’i 24 na farko. Ya ce zai tuntubi shugabannin cibiyoyin lafiya a jihar domin tabbatar da cewa al'ummar Katsina suna amfana da wannan tsari.
A karshe, Kwamanda Lede ya bukaci goyon bayan gwamnatin jihar Katsina wajen kafa kwamitin shawarwari na tsaron hanyoyi, wanda zai hada gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki. Ya bayyana cewa gwamnatoci da dama sun riga sun kafa irin wannan kwamiti a jihohinsu, kuma yana da yakinin cewa gwamnatin Katsina za ta amince da hakan.
Ya jaddada cewa hadurra akan hanya na kashe mutane da dama fiye da yadda mutane ke tsammani, kuma matakin da ya fi dacewa shi ne hada kai domin dakile hakan.
"Na yi imani da irin hangen nesa da jajircewar da na gani a wajen gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda. Ina da kwarin gwiwar cewa idan muka gabatar da bukatar kafa kwamitin, za a amince da shi nan ba da jimawa ba," in ji Kwamanda Lede.