Shugaban Karamar Hukumar Katsina Ya Rantsar da Sakatare, da sauran mukarraban sa.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12052025_190319_FB_IMG_1747076532450.jpg



 Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times 

A ranar Litinin, 12 ga Mayu, 2025, Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Honourable Isah Mikidad AD Saude, ya jagoranci bikin rantsar da Sakataren Karamar Hukuma, Mataimaka, masu Kula da Ayyuka (Supervisory Councillors), da sauran masu rike da manyan mukamai da aka nada domin tafiyar da mulki a matakin karamar hukuma.

An gudanar da bikin a harabar sakatariyar karamar hukumar, inda aka tarbi baki daga sassa daban-daban domin shaida wannan muhimmin biki da zai kara habaka shugabanci da inganta gudanar da ayyukan ci gaba a matakin karamar hukumar da jiha.

Daga cikin wadanda aka rantsar har da Injiniya Abubakar Jafaru Danbaba, wanda aka fi sani da Majidadin Daliban Damagaran, wanda ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin supervisory councilors dake Kula da Ayyuka na yankin Shinkafi B. An bayyana nadin nasa a matsayin wani ci gaba duba da irin gudummawar da ya bayar wajen habaka matasa da ci gaban al’umma a baya.

Bikin ya samu halartar manyan baki masu daraja, ciki har da Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Jihar Katsina, Honourable Bishir Gambo Saulawa, wanda shi ne jagoran siyasa na karamar hukumar Katsina. Haka zalika, Honourable Ali Abu Aliyu Albaba, dan majalisar dokoki ta jihar mai wakiltar karamar hukumar Katsina.

Sauran mahalarta sun hada da kansiloli daga unguwanni daban-daban, dattawa, shugabanni na gargajiya da na siyasa, da kuma fitattun ’yan karamar hukumar Katsina da suka halarta domin nuna goyon baya ga sabbin jami’an da aka nada.

A jawabin da ya gabatar yayin taron, Shugaban karamar hukumar, Isah Mikidad ya bukaci sabbin jami’an da su rungumi gaskiya, jajircewa, da kuma gudanar da ayyukansu cikin kwarewa da amana. Ya jaddada cewa mukaman da aka ba su alhaki ne mai nauyi, kuma ya bukace su da su hada kai domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban karamar hukumar.

An kammala bikin da godiya daga daya cikin sabbin jami’an da aka rantsar, wanda ya bayyana alkawarin aiki tukuru da jajircewa domin cika burin da gwamnatin karamar hukumar ke fatan cimmawa.

Follow Us