A SAKE FASALIN MASARAUTAR KATSINA BISA HUJJAR TARIHI DA CANCANTA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11052025_191850_IMG-20250511-WA0132.jpg



Daga Wakilan Katsina Times

Jaridun Katsina Times sun samu wata takarda da za a gabatar wa Majalisar dokokin jihar Katsina, wadda take bukatar a canza fasalin masarautar Katsina da samar mata wasu Sarakuna masu daraja ta daya, sai mai daraja ta biyu, sai mai daraja ta uku a bisa hujjar tarihi da kuma cancanta.

Takardar, wadda ta kawo hujjar cewa zamani, kuma lokaci ya yi da za a dauko littafin tarihi a duba wanda zai tabbatar cewa zaman girman Katsina mai Sarki daya tilo da daraja ta daya ya wuce. 

Takardar ta kara da cewa, a tarihi gidaje uku suka amso tuta wajen Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodio. Sune Malam Ummarun Dallaje (Allah ya yarda da shi), Malam Muhammudu Na Alhaji (Allah ya yarda da shi) da Malam Ummarun Dunyawa (Allah ya yarda da shi).

Tarihi ya nuna cewa, dukkanin su suna da kasa da suka rika mulkin ta bayan jihadi, kuma dukkanin su sun rika amsar umurninsu kai tsaye daga Sarkin Musulmi ne, ba Sarkin Katsina ba. Sun rika tafiyar da mulkin Katsina a hadaka, yayin da kowanne yana tafiyar da kasar sa. Zuwan Turawa ya kaskantar da su zuwa masu biyayya ga Sarki daya.

Takardar ta ce, lokaci ya yi da wàdannan gidajen za a mayar masu da martabarsu ta cikakkiyar sarauta, kamar yadda yake a tarihi. A nan suka ba da shawarar a ba daya daga cikin su Sarki mai daraja ta daya, sauran biyun a ba su masu daraja ta biyu.

Takardar ta ce, Tarihi ya tabbatar da kasar Kurfi ba ta a cikin daular Katsina. Kasa ce mai zaman kanta, wadda ta rika amsar umurni daga wajen Sarkin musulmi. Har zuwan Turawa ba su taba ’yancinta ba, sai daga baya. Kasar Kurfi a duba matsayinta a tarihi, a ba su Sarki ko mai daraja ta biyu ko daraja ta uku.

Tarkardar ta kara da cewa, kasar Maska, Sarkin da ya kafa ta, Sarkin Maska Bako ya yi zamani da Sarkin Katsina Muhammadu Korau. Kasa ce mai tsohon tarihi, kusan daidai da kasar Katsina. Ya kamata a duba tarihinta da kuma cancantar ta, a ba ta Sarki mai daraja ta daya.

Marubutan suka kara da cewa, tarihi ya tabbatar da cewa Gwamnan Nijeriya na Turawan mulkin-mallaka Lugard ya taba ba Sarkin Dankama, Kaura Amah sarautar Sarki mai daraja ta uku, amma Kaura Amah ya ki amsa. Ya ce shi Kaura ne, kuma jarumi, don haka a bar shi karkashin Sarkin Katsina. Marubutan suka ce ya kamata a mayarwa da kasar Dankama wannan darajar da aka taba ba su na Sarki mai daraja ta uku.

Takardar ta kara da cewa, rawar da Malam Dudi na zuri’ar Danejawa ya taka a wajen kafa kasar, wadanda yanzu sune ke sarauta a yankin Malumfashi da Kafur sun cancanta a yi masu sarauta mai daraja ta biyu.

Marubutan suka ce, duk wadannan abubuwan da suka bayyana a sama suna nan a littattafan tarihi, ba shaci-fadi bane.

Suka kara da cewa, duk Najeriya ba wata masarauta mai girma kamar Katsina da take da Sarki daya, mai daraja ta daya, shi daya.

Jihohi suna duba tarihi da maslahar al’ummarsu, su kara masarautu a yankuna daban-daban. Don haka takardar ta kara da cewa, lokaci ya yi da jihar Katsina za ta tafi da zamani.

Suka kara da cewa, duk duniya kasashe masu tarihi suna kariya da girmama gidajen sarautunsu masu tarihi. Don haka suka ce, lokacin da Katsina za ta maido da martabar wannan tarihin, ya yi. Kuma hakan zai sa hatta tsaro da kudin shiga daga masu bude ido su karu.

Takardar ta ce, ba wani karin kudi da zai karu ga jiha, domin kowace Karamar hukuma ita ke daukar nauyin Hakimanta. Kuma ana cire kaso biyu na kudaden Kananan hukumomi ana bai wa masarauta, kudaden da ba a binciken su ko bin diddigin ya ake kashe su.

Suka ce masarautar Katsina na amsar miliyoyin Naira duk wata, amma har yanzu albashin wasu dogarai a masarautar na karbar kasa da Naira dubu goma.

Takardar ta ce, tun da aka nada Sarkin Katsina da ke sama, akwai yankunan da bai taba kai masu rangadi ba, ya ji wane hali wadannan talakawan nasa suke a ciki. Kuma lamarin na yi ma talakawan yankin ciwo. Don haka duk masarautar da aka yanka za a yi amfani da kudaden da ake cirewa na wannan yankin a bai wa masarautar da ke yankin.

Marubutan suka ce, yin haka zai sa kowane Sarki ya shiga gaba wajen ci gaban yankinsa da al ummarsa. Takardar ta rika kafa hujja da littattafan tarihi da takardun tarihi.

Jaridun Katsina Times sun tuntubi wani dan Majalisar dokokin jihar Katsina a kan me za su yi in wannan bukatar ta zo gaban su? Ya bayyana cewa, bai son a fadi sunan sa, amma su zababbun al’umma ne, don haka duk wata bukata ta jama’a suna tare da ita.

Idan al’umma na bukatarm karin masarautu, za su duba tsarin mulki da dokokin Majalisa, za su yi masu, don su wakilan al’umma ne.

Katsina times 
@ www.katsinatimes.com 
Jaridar taskar labarai 
@www.taskarlabarai.com 
Email; newsthelinks@gmail.com 
 07043777779 08057777762

Follow Us