DA GASKE AN SAMU ZAMAN LAFIYA A WASU YANKUNAN BATSARI DA JIBIYA? ...Gani ya kori!!

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes06052025_122432_FB_IMG_1746530940244.jpg

Daga wakilanmu  @ Katsina times 

Da yawan mutane na tambayar halin da ake ciki a yankunan ƙananan hukumomin Batsari da Jibiya, domin samun abun dogaro da natsuwa ko akasinta, duba da yadda yankunan suka taɓa zama tamkar lahira kusa,  yasa wakilan Katsina Time suka yi tattaki domin gano halin da ake ciki. 
A ranar laraba 30-04-2025 muka kutsa cikin karkara da dazuzzukan da suka yi fama da matsalar tsaro, mun fara shiga ƙauyen Batsarin'alhaji dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari amma baa taradda kowa ba sai kangayen gine-ginensu, saidai akwai manoma cikin gonakai suna sharan gona, a dajin haƙon tali ma ba'a taradda kowa ba sai ruƙuƙin dajin kawai, kuma babu wata barazana, amma a lokacin baya nan ne ake kai kuɗin fansa. 

A ƙauyen Tashar Modibbo mun samu mutane suna ta harkokinsu, kuma sunyi mana kyakkyawar tarba, inda dama mana fura da nono muka sha muka ƙoshi, kuma sun bayyana mana cewa duk inda za mu shiga cikin daji ko karkara babu wata barazana, kuma mun tababatar da haka, domin mun ƙara kutsawa muka ratsa garin muka yi yamma, inda muka je koramar sha da wanka, sannan muka ƙara nutsawa har sola inda akayi sasanci lokacin mulkin gwamna Masari,  sannan  muka isa dajin Baranda, inda muka iske ana aikin haƙar ma'adanai ko zinari, kuma mun taradda manyan gwasake a wajen amma babu wata barazana, kowa na aikin gabanshi Hausawa da Fulani ana ta aiki, masu acaɓa kuma suna jigilar buhunnan kayan da aka haƙo zuwa wajen niƙa, Nahuta.

Daga nan muka kama hanyar Nahuta, inda muka ratsa wani ƙungurmin daji muka shiga ta Garin Liman, sannan muka isa Nahuta muka yada zango inda ake aikin niƙa da wanke zinare a garin Nahuta. Wajen ya zama tamkar wata kasuwa da ta shafe shekaru ana hada-hada, Hausa da Fulani tamkar yan gida ɗaya.

Mun tattauna da mutane daban daban, koda yake basu bamu damar ambatar sunayensu ba, amma wani mazaunin Nahuta ya tabbatar mana cewa, tunda akayi wannan zaman sulhun basu samu wani ƙalubale ba, kuma ko allurarka ta ɓata ko aka dauƙa, da an gayawa manyansu musammun Abu Raɗɗe, to ba tare da ɓata lokaci ba zai sa a gano wanda ya ɗauke ta kuma ya hukunta shi, sannan a baka abunka.

A garin Madogara da Zamfarawa wajen kusan duk ya zama kango sakamakon aikin ƴan taadan daji, amma mun taradda wasu suna gyare-gyare kuma sun bayyana mana cewa a yanzu akwai masu kwana garuruwan kuma a shirye suke su dawo garin da zaran sun kammala gyaran gidajen su.

Wani mazaunin Batsari da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana mana cewa a cikin makon nan aka sace masa garke awaki da suka fita kiwo wajen gari, amma da aka gaya ma Abu Raɗɗe, sai ya baza yaranshi cikin daji da karkara, kuma sunyi nasarar cafke ɓarawon, bayan yayi ma shi hukunci mai tsanani, ya miƙa ma shi awakin shi.

A yanzu kam mun lura duk inda ba'a iya zuwa a da, to yanzu za'a iya zuwa kuma babu wata barazana sai dai akwai masu makamai amma  babu ruwansu da kowa. 

Bincike ya nuna tun bayan wani zaman sulhu da akayi da jam'an tsaron soja da yan bindiga a garin Kofa, wanda su ƴan bindiga suka nema domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin, sauƙi ke ta samuwa, inda manyan dakarun daji suka halarta daga yankin Batsari da Jibiya, koda yake suma Jibiya sun kira irin wannan zama a yankinsu ƙalƙashin jagorancin Abdu Lankai, kuma ana ganin ribarshi a fili. Munbi hanyar Batsari zuwa Jibiya, kuma bamu ga wata barazana ba.
Mun samu tafiya cikin wadannan yankuna da rakiyar wani yaro da ya rika. Nuna mana hanya.
Mun dauko hotuna da bidiyo masu yawan gaske don amfanin masu bin shafukan Katsina times media forum...asha kallo da karatu lafiya
Yadda wannan zaman lafiya ya kankama a wasu yankunan Batsari, Allah ya mayar da jahar Katsina haka baki dayan ta.
Katsina times 
@ www.katsinatimes.com 
Jaridar taskar labarai 
@ www.taskarlabarai.com 
07043777779 08057777763

Follow Us