Kungiyar Manoma ta Kasa (AFAN), reshen jihar Katsina ta yaba wa gwamnan jihar Mallam Dikko Umaru Radda bisa nasarar bude wata katafariyar masana'antar kayayyakin aikin gona da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar.
Shugaban AFAN na jihar, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo ya yi yabon, a zantawarsa da manema labarai a Katsina jim kadan bayan kaddamar da masana'antar.
Gwajo-gwajo ya ce manoman jihar suna matukar alfahari da yadda manufofin gwamnan a fannin noma suka zama abin koyi ga wasu jihohi kuma har hakan ya jawo hankalin shugaban kasa don zuwa kaddamar da aikin.
“Hakika mai girma gwamna, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D, ya fitar da jihar Katsina kunya, AFAN na matukar alfahari da shi a madadin daukacin manoman jihar Katsina.
“Wannan babbar masana'antar ta kerawa da hada kayan aikin gona zata rika hada taraktoci, da injinan huda, da injinan girbi da sauran kayayyakin noma waɗanda manoma a fadin jihar nan zasu rika amfana da su.
“Cibiyoyin za su kuma horar da dalibanmu da matasanmu kan fasahohin aikin gona da suka hada da sarrafa kayan aikin noma na zamani da sauran muhimman bangarori na aikin gona".
Alhaji Ya'u Gwajo-gwajo ya kuma yaba da kishin Gwamna Radda wajen bunkasa samar da abinci ta hanyar inganta ayyukan noma da raba takin zamani da sauran muhimman kayan aikin gona.
“A damina baara, watau shekarar 2024, gwamna ya raba takin zamani Mai yawan tan dubu 448 wanda ya taimaka matuka wajen bunkasa noma a shekarar, ya Kuma bunkasa kasuwanci a kayan amfanin gona.
“Hakazalika a daminar bana, gwamnan zai raba tan dubu 400 na takin zamani ga manoma a fadin kananan hukumomin jihar 34.
"A madadin mambobinmu na kungiyar AFAN, muna mika godiyarmu ga maigirma gwamna bisa wasu tsare-tsare da ya kirkiro da suka hada da tsarin hada kananan manoma zuwa kungiyoyi hadin gwiwa domin ba su talladi iri-iri".
Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo ya Kuma bayyana godiyar kungiyar AFAN ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ministan noma bisa raba injinan ban ruwa da na feshi da na masu girbi da sauran kayan aikin goma guda 4,000 ga manoman jihar bara.
Ya bukaci manoma a jihar da su ci gaba da marawa gwamnatin jihar da ta tarayya baya a kokarin da suke yi na kawo sauyi mai ma'ana a harkar noma a jihar.