NA ZIYARCI KABARIN ANNABI AYUBA (AS) DA DEBO RUWAN RIJIYARSHI.

top-news

@Mawallafin Jaridun 
Katsina Times da Taskar Labarai 
Kwanakin baya nayi wasu tafiye tafiye zuwa kasashe daban daban da  ziyartar wasu wurare masu Tarihi da Albarka da suka shafi Musulmi da Musulunci.
Zan rika kawo wasu hotuna da dan Takaitaccen bayani na wadannan wurare Dana Ziyarta.
A gabashin kasar Iraqi, Kilomita 167 a kwai yanki mai suna Hilla. A garin, mada in, Nan 
Hubbaren Annabi Ayuba ( AS) yake.
Ginin hubbaren ya kumshi Masallaci, Kabari da kuma Rijiyar da  Asalinta, shine Ubangiji yace Annabi( AS)  ya buga kafarsa, Ruwa zai fito ya sha yayi wanka cutar dake jikin shi, zata warke.
Rijiyar Allah ya tsare ta tana nan. Ana zuwa daga koina a kasashen duniya domin sha da dibar ruwan.
Wannan Rijiya mai fiye da shekaru dubu Uku nasha na kuma debo ruwan ta.