Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) har yanzu ba ta saki rahoton bincikenta ba game da zargin badakala da suka shafi tsofaffin Ministocin Jinƙai da walwalar Jama'a, Sadiya Umar-Farouk da Betta Edu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
An kaddamar da binciken kimanin watanni 15 da suka wuce, wanda ya haɗa da tsohuwar Kwamishinar Shirye-shiryen Tallafin Zamani ta Kasa (NSIPA), Halima Shehu da wani dan kwangila, James Okwete.
EFCC ta bayyana cewa binciken har yanzu yana ci gaba.
An rawaito cewa EFCC da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Sauran Laifukan da Suka Danganci Rashawa (ICPC) sun kwato sama da Naira biliyan 30 daga asusun banki 50 da ake da alaka da ma’aikatar lokacin da Edu da Sadiya ke kan mulki.
Matsala ta fara ne ga Edu, Sadiya da wasu manyan ma’aikata a ma’aikatar bayan wata takarda ta bayyana a kafafen sada zumunta inda aka ce Edu ta nemi Akanta-Janar na kasa na lokacin, Oluwatoyin Madein, da ta aika Naira miliyan 585 zuwa asusun wani mutum mai suna Oniyelu Bridget.
Ma’aikatar ta bayyana cewa Bridget tana matsayin Akantan Ayyuka na Shirin Tallafawa Mabukata.
Daga baya wasu takardu da ke nuna cewa Edu ta amince da wasu kudade da ake ganin sun saba da ka’ida, ciki har da na kudin jirgi zuwa jihar Kogi wadda bata da filin jirgi, suka bazu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Edu a ranar 8 ga Janairu, 2024.
Kwana kafin dakatar da Edu, an dakatar da Halima Shehu daga matsayin Shugabar Hukumar NSIPA bisa zargin almundahana, bayan da Edu ta bayyana cewa biliyoyin naira sun ɓace a lokacin da Shehu ke jagoranci.
Bayan haka, EFCC ta kama Halima Shehu don yi mata tambayoyi kan zargin badakalar Naira biliyan 44 daga asusun NSIPA zuwa wasu asusun kamfanoni da na mutane a ƙarshen Disamba 2023.
EFCC ta kuma yi wa Sadiya Umar-Farouk tambayoyi kan zargin cin hanci wajen kashe Naira biliyan 37.1 na kudaden tallafin zamantakewa a lokacin da take minista.
Daily Nigerian Hausa