Shugabanin Sabon Shirin Tallafa Wa Mata "Nigeria For Women Project" Sun Ziyarci Mai Martaba Sarkin Katsina.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes24042025_202222_FB_IMG_1745525974466.jpg

Daga: Muhammad Ali Hafizy @Katsina Times.

Shugabannin sabon shirin tallafa wa mata mai suna "Nigeria For Women Project" karkashin jagorancin shugabar tafiyar Hajiya Rabi Muhammad sun ziyarci mai martaba sarkin Katsina, Dr Abdulmumeen Kabir Usman.

Ziyarar ta wakana ne a ranar Alhamis 24 ga watan Afrilu na shekarar 2025, a kokarin da shugabar ta ke yi wajen kai ziyarori ga iyayen al'umma, duba da cewa al'umma ne za'a yi ma aikin kuma yakamata a sanar da shugabannin al'ummar.

Mai martaba sarkin Katsina, Dr Abdulmumeen Kabir Usman, tare da yan majalisar shi, su ne suka karbi ziyarar, tare da bayyana goyon baya ga shiri, duba da yadda shiri ya yi tanadi domin ganin samar da kyakkyawan sauyi ga al'umma.

Mai martaba sarki, ya shawarci shuwagabannin da dage wa a cikin aiki, ya shaida masu cewa wannan wata dama ce aka basu domin ganin sun taimaka al'umma, ya kara da cewa wannan aikin da zasu yi aiki ne da Allah ya ke so, kuma su bada kokari sosai wajen yin shi.

Follow Us